
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ƙasa TCN, ya ce layin T347 da ke yankin Gombe zuwa Damaturu 330kv da ya lalace a ranar Juma’a ya haddasa katsewar wuta a yankunan Maiduguri da Damaturu na jihohin Borno da Yobe.
Babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Ndidi Mbah a wata sanarwa, ya ce tawagarsu bayan gudanar da bincike sun gano cewa an samu katsewar ne daga tushen layin, wanda hakan yasa ya shafi raba wuta a yankunansa.
Saidai, TCN ya ce duk da ƙalubalen, an samu cigaba da raba wuta a wasu yankuna ta tashar lantarkin Maiduguri ta gaggawa (MEPP) ciki har da Beneshiek, Damasak, Bama, University, Maiduguri, Monguno da sauransu.
Haka kuma, yankin Damaturu da kewayensa zai riƙa samu daga layin Potiskum gabanin a yi gyara ga sashen da ya lalace.
Mbah ya ƙara da cewa, a halin yanzu injiniyoyi suna wajen da ya lalace, inda suke ƙoƙarin gyara a kai domin dawo da yanayin yadda yake a baya.
