Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar Ɗinkin duniya (UNDP) tare da haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Katsina sun shirya taron bita da ƙarawa juna sani a kan dabarun samun zaman lafiya mai ɗorewa a cikin al’umma.
Taron bitar ya ƙunshi masu ruwa da tsaki a tsakanin Fulani makiyaya da manoma a ƙananan hukomomi dake fama da matsalar tsaro a jihar Katsina.
Su dai waɗannan al’ummomi sun fito ne daga ƙananan hukomomin Faskari, Jibia, Batsari, Safana, Ɗanmusa, Ƙanƙara, Matazu da kuma Kurfi.
Yayin taron wanda ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta ɗauki nauyi, an gabatar da ƙasidu masu nuna muhimmancin ƙaunar juna da zama lafiya a tsakanin su.
Wanda suka gabatar da jawabai a wurin taron bitar sun haɗa da kwamishinan ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma Farfesa. Abdulhamid Ahmad Mani, da mai ba gwamna shawara akan harkokin tsaro Hon. Ibrahim Yusuf Safana.
Inda suka bayyana ƙoƙarin da gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa ke yi domin ganin al’umma sun zauna lafiya da ganin sun ci moriyar abinda gwamnati ke yi.
