An tasa ƙeyar tsohon Fraministan Mali zuwa kurkuku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata kotu a Bamako ta yanke wa tsohon Fraministan, Moussa Mara hukuncin shekara guda a gidan yari bisa samun sa da laifin wallafa rubutu a kafar sadarwa da ke goyon bayan ƴan siyasar da aka tsare da nuna gazawar hukumomin gwamnati.

A jiya Litinin yayin hukunci a kotun, wadda ke kula da laifukan da suka shafi yanar gizo ta kuma yi masa dakataccen hukunci na shekara ɗaya da tarar CFA 500,000, wato kimanin Dala 887.

Mara, wanda shi ne fraministan ƙasar daga shekerar 2014 zuwa 2015, ya shiga hannun hukuma ne a ranar 1 ga watan Agusta bayan wallafa rubutun inda a ciki ya ce ya ziyarci fursunoni ƴan siyasa a kurkuku tare da cin alwashin nema musu adalci.

Masu tuhumar sa sun ce kalaman nasa yunƙuri ne na ƙalubalantar halascin aiki da doka da kuma samar da rashin yarda ga jagorancin gwamnatin sojin ƙasar.

Mali tana ƙarƙashin mulkin sojoji tun bayan juyin mulki guda biyu da aka gudanar a ƙasar a shekarun 2020 da 2021.

By Babaji