Alassane Ouattara ya lashe zaɓen Ivory Coast karo na huɗu

Spread the love

Shugaban ƙasar Côte d’Ivoire, Alassane Ouattara mai shekaru 83, ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa domin yin wa’adin mulki na huɗu bayan samun kaso 89.77 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen ƙasar.

Hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da sakamakon a ranar Litinin, inda ta ce nasarar Ouattara ta biyo bayan hana manyan abokan takararsa biyu shiga zaɓen.

Masana harkokin siyasa na ƙasar sun ce wannan sakamakon ya nuna ƙarfin jam’iyyarsa mai mulki da tasirinsa, duk da cewa wasu ƴan adawa suna kalubalantar tsarin gudanar da zaɓen.

Rahotanni sun ce wasu ƙasashen ƙetare da ƙungiyoyin sa ido na duniya na aikin sa ido kan yadda za a tafiyar da rikice-rikicen siyasa da ka iya tasowa bayan bayyana sakamakon zaɓen.

By Babaji