Ƙaramar Hukumar Katsina za ta gina cibiyar kula da lafiyar mata masu juna biyu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wannan cibiya idan an kammala ginawa za ta zama na farko a ƙaramar hukumar kuma ana sa ran za ta magance matsalar ƙarancin cibiyoyin kiwon lafiya a yankin.

Haka kuma zai inganta samun damar yin amfani da cibiyoyin ga mata da yara ƙanana.

A cewar shugaban karamar hukumar, Alhaji Ishaq Miƙidad cibiyar za ta riƙa samar da cikakkiyar kulawa ga mata tun kafin su haihu da kuma bayan sun haihu, domin tabbatar da cewa suna samun tallafi yadda ya kamata a dukkan matakan haihuwa. “Haka kuma, za a riƙa gudanar da shirin rigakafi da tarurrukan wayar da kai kan lafiyar yara da abinci mai gina jiki domin ilmantar da iyalai a wannan cibiyar kiwon lafiya,”Inji shugaban ƙaramar hukumar.

Shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar wa al’ummar karamar hukumar Katsina cewa zai yi iya yin sa na samar da ababen more rayuwa a saƙo da lungu kamar yadda ya yi alƙawari a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Mazauna unguwar sun nuna jin daɗin su da samar da wannan cibiya da suka ce zai sauƙaƙa masu wajen wahala tafiya mai nisa da ɓata lokaci wajen samun kulawa a wasu manyan asibitocin da ke Katsina.

Sunyi kira ga shugaban ƙaramar hukumar da ya samar da isassun kayan aiki da suka haɗa da likitoci, unguwar zoma da sauran kayan aiki a cibiyar.

By ukarofi