Gwamnan Taraba na shirin komawa APC

Spread the love

Mai Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas shawara akan harkokin siyasa Josiah Kente ya bayyana cewa kiran da ake yi wa gwamnan na ya koma jam’iyyar APC zai taimaka matuƙa wajen haɓaka cigaban jihar.

Kente ya ce, shigar gwamnan cikin jam’iyyar mai mulki a ƙasa zai buɗe sabbin hanyoyi na haɗin gwiwa da samun tallafin gwamnatin tarayya, sannan ya taimaka wajen inganta ayyukan raya ƙasa a jihar.

Ya ƙara da cewa, al’ummar jihar suna sa ran ganin ci-gaba kuma hakan zai fi yiwuwa idan aka samu daidaiton siyasa tsakanin gwamnatin jiha da ta tarayya.

Kazalika, ya kiraye masu ruwa da tsaki a jihar da ƙungiyoyin al’umma da matasa da su kasance masu goyon bayan gwamnan akan abinda ya kira da “sake haɗewa akan bunƙasa da nasarori”.

Tun bayan dawowar mulkin dimukraɗiyya a shekarar 1999, jam’iyyar PDP ce take mulki a jihar, inda ake ganin komawar Kefas APC ka iya sauya akalar siyasar jihar na tsawon lokaci.

By Babaji