Gwamnatin Tarayya za ta karrama ƴan jaridar da suka wayar da kan jama’a akan sauya fasalin haraji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Tarayya ta sanar da ƙaddamar da kyautar karramawa ga ƴan jaridar da suka ruwaito ingantaccen rahoton bayanin sauya fasalin haraji da masu wayar da kan al’umma wajen bada bayanai na gaskiya a kai.

Shugaban kwamitin gyare-gyaren tsarin kasafi da haraji, Taiwo Oyedele ya sanar da haka a ranar Talata ta kafar X, inda ya ce Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu akan ƙudirorin haraji guda huɗu da za su fara aiki daga ranar 1 ga wata Junairun 2026.

A cewar sanarwar da ya wallafa, za a bada kyautar ne da nufin inganta harkokin tattaunawa da al’umma, yaƙi da ruɗar da al’umma ta hanyar labaran bogi da kuma ɗaga darajar aikin jarida da ya mayar da hankali wajen bayanin haraji yadda al’umma za su fahimta kuma su gamsu.

Haka kuma, kyautar ta taƙaitu ne ga ƴan jarida da ke aiki a Nijeriya a gidajen jarida, rediyo da talabijin da kafafen sada zumunta da waɗanda ke ƙoƙarin wayar da kan al’umma a kai.

Ya ce, za a bada kyautar ne ga waɗanda suka yi aiki akan batun daga ranar 1 ga wsta Yuli har zuwa 31 ga watan Disambar 2025, sannan za su miƙa shi ne ta ɗaya daga cikin yarukan nan; wato Turanci, Pidgin, Hausa, Igbo ko Yaroba.

Ya ƙara da cewa, wanda ya zo na ɗaya zai samu kyautar Naira miliyan 10, sai na biyu zai samu miliyan N5, sannan miliyan N3 ga wanda ya zo na uku.

Kazalika, ya ce za a bude shafin https://fiscalreforms.ng domin karɓar bayanan waɗanda ke neman samun kyautar a ranar 31 ga watan Disambar 2025.

Domin neman ƙarin bayani za a iya tuntuɓa ta adireshin yanar gizo kamar haka; [email protected] ko kuma lambar waya 08109753151.

By Babaji