Shin waye Ouba Ali na Kamaru?

Spread the love

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Kamar yadda na bayyana a rubuce-rubucena da suka gabata, ’yan kwangilar rusa Arewa da yaƙi ta hanyar kunna fitinar ƙabilanci, su na nan a ciki da wajen Nijeriya. Kama daga yara ‘yan soshiyal midiya zuwa gagga masu ɗaukar nauyin aikin. Ouba Ali Mohaman jigo ne ko uban gida ne ga ’yan kwangilar nan na Nijeriya. Dan Jamhuriyar Kamaru ne da bayanansa su ka nuna ya na zaune a babban birnin ƙasar Yaounde amma asalinsa daga Tibati ne a nan Kamaru. Ya yi tafiye-tafiye ƙasashe ciki kuwa da Amurka inda a 2018 ma ya shiga Washington DC har ya gana da wasu ’yan jarida. Tibati da ke zama gida a wajensa na da rinjayen Fulani mazauna sai ƙabilar da ta yi ruwansa Mbum mai masarautar Bamun. Wannan mutumin shi ke zama babban mai goya ‘yan kwangilar rusa Arewa da amfani da baƙaƙen maganganu wajen aibanta Shehu Mujaddadi da kalmomin ingiza al’ummar Arewa su shiga yaƙin ƙabilanci. Bayanansa a fili su ke a yanar gizo inda ya kan yi rubutu da sukar manyan malamai masu daraja da tasiri. In ka bi sawun ‘yan kwangilar nan su kan shiga Kamaru kuma ina ganin biri ya yi kama da mutum don su na da Kartagi uban ‘yan caca. Abun damuwa a samu wani daga Kamaru ya wuni ya na sharhi kan lamura masu hatsari da za su iya ta’azzara lamuran taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya.

Abun da ya fi ɗaukar hankalina shi ne Marwa ko Maroua Maitatsine daga Kamaru da ya shigo Nijeriya ya haddasa kisan gilla ga mutane bila-adadin wasu ma ta hanyar yankan rago. Kanawa, Barnawa, Adamawa da Gwambawa za su fi sanin labarin wanda mugun mutumin mai wa’azin kala-kato da ya jagoranci ta’addanci a garuruwanmu na Arewa. Akasari yara ‘yan bana bakwai ba su san me ya faru ba, amma an zo a na murɗe wuyan tarihi a soshiyal midiya inda kowane mai rubutun ganin dama zai hau ya rubuta abun da ya ga dama. Ouba Ali Mohaman na layi mai hatsarin gaske don irin bayanan da ya ke yaɗawa. Mutumin da ke da’awar shi farfesa ne amma ba shi da aiki sai daurewa masu kunna wutar ƙabilanci baya da iza wutar aibanta jagorori masu daraja a Nijeriya irin Shehu Mujaddadi, Sir Ahmadu Bello da sauran manyan malaman Islama. Mutumin nan da ke Kamaru amma hankalinsa ya na kan arewacin Nijeriya da ya ke aikin kunna wutar fitinar ƙabilanci. Hakika tamkar ga masu tattara kirare a Arewa amma ga mai ashana can a Kamaru. Kafin ashana ta iso, ya dace hukumomi su taka ma ta birki. Ko da ba huldar babban zumunci tsakanin Nijeriya da Kamaru kan wasu lamura da su ka hada da mikawa Kamaru yankin Bakassi, ƙwallon ƙafa da sauransu, amma dai makwabta a ke kuma ba yanda a ka iya sai dai a nemi hanyoyin zama lafiya da juna.

Har wata ƙungiya ta farafaganda ya ke kanbamawa wai “Hausa Hackathon” da ke da lambar sadarwar salula ta ƙasar Faransa. Mun san cewa Faransa ta mara baya lokacin da Odumegwu Ojukwu ya aiyana kafa kasar Biyafara a 1967. Don haka ba mamaki ka ga ‘yan kwangilar nan na ƙururuwar lallai sai a sake Nnamdi Kanu mai IPOB da a ke zargi da cin amanar ƙasa da ta’addanci. Hausa Hackathon har lambar yabo ta ke damkawa wanda ya yi fice  a harkar kwangilar da a ka tabbatar ta rusa Arewa ce.

Ouba har kartar kasa ya ke yi ta rashin girmamawa ga shugaba Bola Ahmed Tinubu wai ya biya diyya ga waɗannan masu iƙirarin karyar kare Hausawa Naira tiriliyan 900!. In mun yi lissafi da kasafin kuɗin Nijeriya na bana Naira tiriliyan 54.9 a matsayin mizani, ya nuna diyyar za ta kai kimanin kasafin kuɗin Nijeriya na shekaru 17. Tun da Ouba ya dau kan sa a matsayin madugu na waɗannan ‘yan kwangila har ya na maganar diyya, sai ya bayyana ma na shin shi za a ba wa diyyar ya raba ko zai zo a tawagar su kanwa uwar gami don karɓar makudan kuɗin nan. A ina ma a ka taba yin irin haka wani ya fito daga wata kasa ya aza gwamnatin wata kasa neman biyan diyya kan alƙaluman son zuciya.

Zan yi amfani da wannan dama wajen kira ga gwamnatin Nijeriya ta buƙaci gwamnatin Jamhuriyar Kamaru ta miƙo ma ta wannan mutumin don gudanar da bincike kan ayyukan ingiza matasa da ya ke yi da ka iya kunna gagarumar fitina a Arewa. Na tabbata akwai bayanai a kan Ouba da waɗanda ya ke hulɗa da su a nan Nijeriya. In ba mugunta ba, me zai sa wani da ke zaune a Kamaru ya riƙa cillo harshen wuta cikin Nijeriya. Ba mu son fitina da kowa. Nijeriya uwa ce a Afurka kuma duk wani ɗan Afurka musamman a Afurka ta yamma ya san zaman lafiyar Nijeriya salama ne ga daukacin yankin ECOWAS/CEDEAO mai ƙasashe 15 gabanin ɓallewa a siyasance ta Nijar, Mali da Burkina Faso.

A ƙarshe kowa ya zauna lafiya shi ya so. Kar wani ya ga ya na hawa soshiyal midiya ya na zage-zage kuma ya kwana lafiya, hakika wataran mai karambani zai gamu da hushin hukuma. Ai ba wani ‘yancin faɗar ra’ayi da ya ba wa wani dama ya muzanta wani shugaba da bakin fenti kuma ya yi tunanin banza ta sha. Ba wanda ya hana kowa faɗar ra’ayinsa amma ba ta hanyar cin mutunci ko cin zarafi ba. Duk wanda bai san haka ba, ya tambayi masana shari’a da ya yarda da su, su yi ma sa bayani na iyakokin hurumin faɗar ra’ayi. Ko dai jagororin waɗannan ‘yan kwangila su ja birki ga ‘yan barandarsu ko kuma doka ta yi aikinta.

Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah kuma ko bai san Allah ba ya san kuliya manta sabo.

Duk da wasu majiyoyi na tabbatar da Ouba ba lallai farfesa ba ne kawai tan a yiwuwa ya na iƙirari ne; ba za mu shashantar da batun sa haka kurum ba don rawar da ya taka ta kangarar da wasu matasa a Arewa  a tsawon lokaci ba a bar kyalewa ba ce. Ba mugun abu irin rainon ‘ya’yan macizai da ba makawa ranar da su ka girma ba za su manta gadon guba daga iyayensu ba. Gaskiya ne Ouba ya yi wuf ya rufe shafinsa na yanar gizo na fesbuk kamar yanda akasarin yaransa su ka yi don ka da a samu cikakkun bayanai kan wainar da su ke toyawa, amma duk wasu muhimman bayanansa na nan mu na nazari a kan su. Ouba gara ya ma bude shafinsa ya ci gaba da yayata ayyukan da ya ɗaukar kan sa, ya fi sauki da ya saje da ‘yan lakada-kawas wajen shiga sunkuru. Haƙiƙa da shi da mutanen da ke bin da’awarsa na bin hanyar da ba za ta ɓulle ba. Ashe da haka zai shirya taro har da kurin gayyatar UNESCO kamar yadda ‘yan kanzaginka ke yayatawa?. Duk wanda zai shirya gagarumin taro na duniya don bitar tarihin babbar al’umma irin Hausawa ba daidai ba ne kuma ya ɓoye kan sa don ba buƙatar nuƙu-nuƙu a wannan muhimmin aiki.

Rufe shafin kaɗai na nuna cewa dama kamar rashin gaskiya a ke ƙullawa da amfani da hanyoyi na dabaru. Yadda ka ke amfani da sayarda sunan Hausawa don yiwuwar shugaban Kamaru Paul Biya ya ba ka muƙami, ba hikima ba ce, ka faɗaɗa aikin har da ƙetarowa cikin Nijeriya. Neman haddasa fitina da za ta iya jawo targaɗen diflmosiyya ba zai yi ma ka kyau ba. ƙarshe za ka zama ba ka nan ba ka can. Kowa zai ɗaukeka za ka iya ƙulla ma sa makirci don haka ba zai yarda da kai ba. In ma ba rashin dogon tunani ba ka cillo harshen wuta Nijeriya amma ka miƙa fetur ɗin hannun ‘yan bazata ko mutanen da ke nuna ɗabi’ar ‘yan fasa ne kowa ya rasa. Nan gaba in za ka samu wata damar ka rika bincike sosai kafin zaɓar abokan tafiya don manyan masu sharholiya na cewa in za a ci naman da ba a yanka ba, a ci mai maiko. Haba kai ma kawai ka ɗauko wasu da ba su da takamemmen aiki sai yaɗa farafagnda a yanar gizo ai ba za a haifar da sakamako mai ma’ana ba don akasarin abubuwan da su ke rubutawa shaci-faɗi ne da ba tushe balle madafa.

Kammalawa

Jama’a da yardar Allah akwai bayanai rututu na haska mutanen nan da ba sa tafiya kan hanya mai alheri. A kasance da mu kuma mun yi alwashin tabbatar da adalci da kawo sahihan bayanai. Kishin ƙasa ma ya zama wajibi ga duk ɗan ƙasa nagari. Ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya kuma a Nijeriya ba mu da gida da ya fi Arewa albarka. Don haka ba za mu naɗe hannu mu bar wasu masu bahaguwar manufa su kawo ma na fitina ba. Da musulmi da mabiya addinin Kirista na zaune lami lafiya tsawon shekaru a tsohon Lardin Arewa. Tarihin jagorancin Firmiya Sir Ahmadu Bello ya tabbatar da haka. Kar mu bari wasu masu ƙin jinin salama su haddasa ma na wutar fitina da ruwa ba zai kasha ta nan take ba. Allah ya kiyaye.

By ukarofi