
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani tsohon mataimaki ga shugaban ƙasa mai suna Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa gwamnatocin wasu ƙasashe na ƙoƙarin haddasa fitina a Nijeriya.
A wani rubutu da ya wallafa a dandalin Facebook da yake tsokaci akan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump cewa Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ake da damuwa akansu, Baba-Ahmed ya kirayi al’ummar Nijeriya da kada su samu rarrabuwar kai a sanadiyyar rahotannin, waɗanda ake nufin cutar da Nijeriya da su.
Ya ce, cewa ana yi wa al’ummar Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ya saɓa wa haƙiƙanin abinda ake gani a zahiri, wanda sanannen abu ne cewa rashin tsaro a wasu sassan ƙasar ya shafi Musulumi da Kirista.
Ya kuma zargin Donald Trump da masu goyon bayansa akan ikirarin da ƙoƙarin cimma wata ɓoyayyar manufa, yana mai cewa Amurka tana yi wa ƙasashen Afirka hassada bisa yawan al’umma da ƙarfin tattalin arziƙi musamman irin su Nijeriya, Sudan, Libiya da Afirka ta Kudu.
Kazalika, ya alaƙanta zargin shugaban Amurkan da matsayar Nijeriya akan lamuran ƙasa da ƙasa musamman ayyukan sojoji a Gaza da neman a ba Afirka kujerar ta musamman a majalisar tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
