Daga DAUDA USMAN a Legas
Wani shahararren ɗan kasuwa mazaunin Legas, Alhaji Ummaru Muhammed Yola, asalin Jihar Adamawa, ya bayyana cewa Kasuwa ta Mile 12 Intanashinal Maket ta zama babbar kasuwa wadda ta fi sauran kasuwannin nahiyar Afirka girma da tasiri, musamman wajen harkar saye da sayar da abinci kamar wake da shinkafa.
Alhaji Ummaru, wanda yake ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kasuwar Mile 12, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam (Sardaunan Egbaland), yana riƙe da muƙamin Shugaban Sashen Cigaban Harkokin Kasuwancin Wake da Shinkafa. Ya bayyana haka ne bayan kammala bikin walimar bude sabon gidansa da ya gina a unguwar Mile 12, ranar Lahadin da ta gabata.
Taron walimar ya samu halartar manyan baki daga Jihar Adamawa, ciki har da Hajiya Halimatu Umar (kanwar mahaifiyarsa) daga Mayo Belwa, Alhaji Rufa’i Jada, Alhaji Nasiru Ofisa, da wasu ‘yan uwa da abokansa. Haka kuma an samu halartar jiga-jigan kasuwar Mile 12, ciki har da Sakataren Dattawan Kasuwa, Alhaji Abdulwahab Tsoho Babangida, da shugabannin sassa daban-daban na kasuwar.
A cikin jawabinsa, Alhaji Ummaru ya bayyana cewa Mile 12 Intanashinal Maket ta kai matsayin da ake zuwa daga ƙasashen ketare irin su Niger, Benin, da Chadi, domin gudanar da kasuwanci, saboda amincinta, tsarinta, da nagartar shugabancinta.
A cewarsa, “Kasuwa ta Mile 12 ta wuce kasuwanni da dama a nahiyar Afirka. Wannan nasara ta samu ne saboda jajircewar shugabanmu, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam, wanda Allah Ya bai wa hikima, hangen nesa da kuma kwarewa wajen jagoranci.”
Ya kara da cewa, karkashin shugabancin Alhaji Shehu Usman Jibrin, kasuwar ta samu ci gaba mai ɗorewa ta fuskar tsaro, tsabtace muhalli, da tsarin cinikayya na zamani.
“Kasuwar tana ƙara bunƙasa kowace rana saboda shugabanni masu hangen nesa da kishin al’umma. Wannan ya sanya ta zama ginshiƙin harkar abinci a Nijeriya da ƙasashen makwabta,” inji shi.
A ƙarshe, Alhaji Ummaru ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da kare kasuwar da al’ummar da ke cikinta, tare da fatan Nijeriya ta ci gaba da samun zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki.
