Gwamnatin Kaduna za ta ɗauki sabbin ma’aikatan lafiya 9,000 a tsawon shekaru biyar masu zuwa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin jihar Kaduna za ta ɗauki sabbin ma’aikatan lafiya 9,000 cikin shekaru biyar masu zuwa.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kaduna Ahmed Maiyaki ya sanar da haka a zaman da ya yi da manema labarai a garin Kaduna ranar Lahadi.

Hukumar Inshorar Lafiya na jihar KADCHMA tare da haɗin gwiwar ƙungiya mai zaman kanta ‘Lafiya: UK-Nigeria Partnership for a Healthier Future’ suka shiya taron.

Maiyaki ya ce zuwa yanzu gwamna Uba Sani ya amince a Karo jami’an lafiya 1,800 domin inganta fannin lafiyar jihar.

“Gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar jami’an lafiya daga nan zuwa shekaru 5 masu zuwa domin inganta cigaban fannin lafiyar jihar.

Ya ce wannan gwamnati tun a shekarar 2023 zuwa yanzu gwamnati ta ɗauki inganta fannin lafiyar jihar da muhimmanci.

“Gwamna Uba Sani ya ce gwamnatin sa za ta riƙa ƙoƙari wajen ganin ta ware sama da kashi 15% daga cikin kasafin kuɗinta na shekara ga fannin kiwon lafiya.

Maiyaki ya ce gwamnatin jihar ta yi ƙoƙari wajen ƙara yawan albashin jami’an lafiya wanda hakan ya taimaka wajen karkato da hankalin kwararrun ma’aikata zuwa fannin lafiyar jihar.

“Yanzu kwararrun jami’an lafiya har rige-rige suke yi a basu aiki a Kaduna saboda inganta albashin ma’aikatan lafiya da gwamna Uba Sani ya yi. Dalilin haka jihar ta zama kan gaba a jihohin Arewa 19.

Kwamishinan ya yi kira manema labarai da su taimaka wajen wayar da kan mutane domin inganta lafiyar mutane a jihar.

By ukarofi