Yanzu muna da ƙaƙƙarfar dokar gurfanar da masu haddasa rushewar bankuna – NDIC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Inshorar Masu Ajiyar ta ƙasa (NDIC) ta bayyana cewa yanzu tana da ƙaƙƙarfan doka wacce za ta ba ta damar gurfanar da masu hannu a rushewar bankuna cikin ƙwarewa da ƙarfi, bisa sabon tsarin doka da aka amince da shi.

Shugaban hukumar, Thompson Oludare Sunday, ne ya bayyana haka lokacin da yake karɓar tawagar ƙungiyar Masu Kula da Farfaɗowar Kasuwanci (BRIPAN) ƙarƙashin jagorancin shugaban ta, Chimezie Victor Ihekweazu (SAN), a hedikwatar NDIC da ke Abuja.

A cewar Sunday, sabuwar dokar NDIC mai lamba 30 ta shekarar 2023, tare da dokar Bankuna da ƙungiyoyin Kuɗi ta shekarar 2020 (BOFIA), ta ƙarfafa ikon hukumar wajen tafiyar da batutuwan rushewar bankuna da kuma gurfanar da waɗanda ke da hannu a haka.

Ya ce, a da, rashin isasshen kariya ta doka kan wannan fanni ne ya sa wasu ke kuɓucewa hukunci duk da irin ɓarnar da suka janyo.

Shugaban NDIC ya gode wa Majalisar Dattawa bisa matakin gyara tsohon tsarin da ke hana hukumar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Haka kuma ya yaba wa kotuna bisa ƙwarewar da suke ƙara samu wajen shari’o’in da suka shafi ajiya da harkokin rushe bankuna, abin da ya taimaka wajen samar da adalci ga masu ajiya.

“Sabbin dokoki da aka ƙara ƙarƙashin NDIC Act 30 na 2023 da BOFIA 2020, tare da fahimtar da kotuna ke samu, sun sa yanzu babu wanda zai iya fakewa da doka don kauce wa hukunci,” inji Sunday.

“Yanzu mutane da kansu ke zuwa hukumar don sulhu kafin a kai kotu — ba wai saboda doka ta kama su ba, amma saboda sun ga yadda dokar ke ƙara matse su.

Sunday ya kuma danganta nasarar hukumar wajen iya tara kadarorin da suka sa aka biya masu ajiya na tsohon Heritage Bank cikin shekara guda da rushewar bankin, ga tasirin wannan sabuwar doka

Ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da amfani da waɗannan dokoki tare da haɗin gwiwa da BRIPAN da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ingantaccen tsarin aikin ta.

A nasa jawabin, shugaban BRIPAN, Chimezie Victor Ihekweazu (SAN), ya bayyana yadda ƙungiyar ta yi aiki wajen haɗa dukkan dokokin da suka shafi rushewar kamfanoni da farfaɗowar kasuwanci cikin tsarin guda ɗaya, wanda hakan ya inganta harkokin warware bashin da kuma sake farfaɗowar kasuwanci a Nijeriya. Ya jaddada muhimmancin ƙarin haɗin gwiwa tsakanin BRIPAN da NDIC wajen gina ƙwarewa da ƙarfafa tsarin gudanar da lamuran kuɗi a ƙasar.

By ukarofi