Tsakanin talauci, rashin ayyukan yi da tsaro

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Daya daga cikin muhimman kanun labaran da suka fi ɗaukar hankali cikin waɗannan ’yan makwannin shi ne batun mutuwar matasa 37 a wajen da suke a tsare a ofishin jami’an Sibil Difens na Jihar Neja. Wannan mummunan al’amari da ya faru ya ɗaga hankalin ’yan Nijeriya da dama, musamman ma iyaye, saboda akasarin matasan da suka rasa rayukansu yara ne, waɗanda ko makarantar sakandire ba su kammala ba.

Hujjar da jami’an Hukumar Sibil Difens ɗin saka gabatar ita ce, an kama su ne saboda suna aikin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba. Amma zarge-zarge sun yi yawa kan sakaci, mugunta, da ƙoƙarin nuna son zuciya wajen ganin sun samu kuɗaɗe masu yawa daga hannun yaran da aka tsare ko iyayensu, da sunan kuɗin beli.

Yayin da gwamnati ke cewa tana gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwar waɗannan yara da kuma gaskiyar zarge-zargen da ake yi musu, muna fatan kuma za ta yi da gaske wajen magance sauran matsalolin da ke angiza matasa shiga ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba. Da kuma tabbatar da ganin ta kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da ake dangantawa da ayyukan haƙar ma’adinai. 

Binciken masana harkokin tsaro da tattalin arziki ya tabbatar da alaƙar da ke tsakanin aikin ma’adinai da tsaro, musamman rigingimu irin na addini da ƙabilanci, da kuma ayyukan ta’addanci na ’yan bindiga masu garkuwa da mutane. 

A wasu rahotannin da gwamnati ke fitarwa ya danganta ayyukan ma’adinai da taɓarɓarewar tsaro da ake fuskanta a wasu yankuna na ƙasar nan. A jihohi irin su Zamfara, Kaduna, Katsina, Taraba, da maƙwaftansu, yadda ’yan ta’adda ke sanya haraji kan waɗannan ma’aikata, suna karɓar maƙudan kuɗi a wajen su. Suna kuma amfani da waɗannan dazuka a matsayin sansanonin ajiye mutanen da aka yi garkuwa da su, ko inda ake shirya ta’addanci da satar shanu. Wani rahoto da Majalisar Dattijai ta fitar ya bayyana yadda ake amfani da kuɗaɗen da ake samu a harkar ma’adinai ana sayen makamai, waɗanda ake amfani da su ana kai hare-hare kan ƙauyuka da makarantu da manyan hanyoyi, domin cutar da jama’a. 

Sai dai bayan haka kuma an tabbatar da cewa akasarin masu aikin haƙar ma’adinai leburori ne matasa majiya ƙarfi dake neman abin da za su ciyar da iyalinsu, kuma su rufa wa kansu asiri. 

Na taɓa shiga wani ofis don in zanta da wani babban jami’i, sai na yi kaciɓin da wani matashi da ya yi wata kyakkyawar shiga cikin kaya masu mutunci da kima. Yana ganina sai ya nufo inda nake cikin fara’a da girmamawa ya gaishe ni, amma sai ya lura da yanayi na kamar ban gane shi ba, duk kuwa da na yi masa kallon sani, amma na manta da ina na san shi. Da ya fahimci haka sai na ga ya yi murmushi ya sosa ƙeyarsa ya ce da ni. “Na san ba ka gane ni ba. Ni ne wanda muka yi hira da kai a wajen da ake aikin haƙar ma’adinai, lokacin da gwamnati ta sanar da rufe wajen da muke aiki, da sunan ba da amincewarta muke aikin ba.” Na biye masa muka fashe da dariya.

Sai a lokacin ne na tuna da shi. Lallai yana cikin matasan da na tarar suna zanga-zanga a bakin titi kusa da wani wajen aikin haƙar kuza a Jos, sun yi busu-busu da ƙura saboda shiga loto. Sun ce sun taru ne don bayyana ɓacin ransu game da matakin da gwamnatin Jihar Filato ɗauka a lokacin na rufe wuraren ayyukan ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Na ce masa, sai kuma ga shi na ganka tsaf-tsaf, kamar ba kai ba. Ya ce, “To, ai Yallaɓai zama a nan ba zai yiwu ba, don yadda abubuwa suka lalace, dole ce ta sa muka bazama nema, don mu samu abin rufa wa juna asiri.”

An gano cewa, ba a Nijeriya kaɗai ba, fiye da mutane miliyan biyu ne suke aikin ma’adinai a tsakanin ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar. Ana waɗannan ayyuka na leburanci ne domin neman ma’adanin zinare, kuza, kwalli, da wasu duwatsu masu daraja da ake amfani da su wajen sarrafa wasu muhimman abubuwa masu kima da martaba. Duk da haɗarin da aikin ke tattare da shi, miliyoyin matasa ne a kowacce rana ta Allah suke barin ƙasashen su, garuruwansu, da iyalansu, domin zuwa aikin leburanci a wuraren da ake aikin haƙar ma’adinai, da nufin nema wa kansu mafita a rayuwa.

Talauci, rashin ayyukan yi, da lalacewar ɗarajar Naira, sun sa magidanta masu ƙaramin jari da ƙananan sana’o’i, suna rufe wuraren kasuwancinsu, suna tattara ɗan abin da suka samu, suna shiga harkar ma’adinai, domin kuɗin da ake sa ran ana samu. Yayin da wasu Allah ke tarfa wa garinsu nono, wasu kuwa a wahale suke ƙarewa. Kamar dai waɗannan matasan yara da suka rasa rayukansu a hannun jami’an rundunar Sibil Difens a Neja.

Abin tausayi ne da takaici, duk da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta za ka ga ɗaruruwan matasa majiya ƙarfi suna shiga surƙuƙin dazuka da kayan tono suna haƙa ramuka masu haɗari, da sunan neman ma’adani. Sannan ɗan abin da aka samu shi za su je su sayarwa wani ci ma zaune da ke gefe ya saya a wulaƙance ya basu abin da ya ga dama. Shi kuma abin da ya tara ya kai wa manyansa da ke birni a zaune su saya, a bashi abin da za a bashi. Shi ya sa dole waɗannan yara su cigaba da zuwa nema, saboda suna sana’a suna ƙara wahala, sai ƙalilan da Allah ya sa suke da rabo.

Babbar ayar tambaya a nan ita ce, su waye ke cin riba da wannan harka ta ma’adinai? Gwamnati ce ko manyan dillalai? Mene ne makomar matasanmu da ke kashe kansu suna neman abin rufin asirin rayuwa?

Ya kamata gwamnati da jami’an tsaro su bibiyi wannan harka a sa ido a kanta sosai. A bibiyi waɗanda suke zuba jari a harkar suke ɗaukar nauyin ’yan ta’addan da suke tsaron wuraren suna yi wa mutane fashin halalin su, da haƙƙoƙin su; waɗanda akasarin su ’yan kasuwa ne, ko ’yan siyasa, da masu riƙe da manyan muƙaman gwamnati. Mutanen da ake zargin su ne ke aiki da manyan masu jigilar wannan ma’adinai zuwa ƙasashen waje inda ake sarrafa su.

A maimakon gwamnati ta zama tana farautar yaran da ke zuwa neman ɗan abin da za su ci, kuma su kula da iyalansu, waɗancan manyan dake ci da gumin matasan ya kamata ta bincika, a ɗauki matakin doka a kansu, musamman waɗanda ke aiki ba tare da cikakkiyar rijista ba. Ya kamata wannan mummunan abin da ya faru na mutuwar matasa 37 a Jihar Neja ya zama mana izina, kuma gwamnati ta tsaya tsayin daka don ganin ta kawo ƙarshen wannan ɗanyen aiki.

A fitar musu da kyakkyawan tsari. A yi musu rijista. A kafa musu ƙungiyoyi da za su taimaka wa kawunansu su tsare musu haƙƙoƙin su, da wayar musu da kai. A riƙa shirya musu bita da horarwa ta yadda za su fahimci kimar abin da suke yi, da darajar arzikin da suke samarwa. A samar musu da tsarin inshorar kula da lafiya, da yadda za su riƙa aikin ba tare da lalata muhalli ba. 

A binciki ’yan kasuwar da ke saye da sayar da waɗannan ma’adinai, har yadda suke fitar da su waje, da gano waɗanda ke amfani da wannan harka suna ƙara arzuta kansu ta haramtacciyar hanya, ba tare da gwamnati, ko al’ummar wannan yanki da suke aiki, suna amfana da arzikin da Allah Ya ajiye musu a yankin ba. 

Gwamnati ta tilasta wa manyan turawan da ke zuwa suna zuba jari a harkar lallai su zo nan ƙasar su kafa kamfanonin sarrafa ma’adinai suna ɗaukar matasa aiki suna samun albashi mai tsoka cikin mutunci.

Ya kamata gwamnati ta yi la’akari da cewa, idan ta takura wajen hana matasa aikin da suke yi na haƙar ma’adinai, da daman su za su koma aikin da bai kamata ba ne, kamar ɗaukar makamai suna ta’addanci, da garkuwa da mutane don samun kuɗin fansa. Saboda sun saba da samun kuɗaɗe suna kashe wutar gabansu. Amma idan aka yi musu tsari mai kyau zai zama an daƙile ayyukan laifi, an kuma sa ido don kada ɓatagari su yi amfani da su.

By ukarofi

Leave a Reply