Ba gajiya da zama ‘yan Katsina ba ne ya sa muke neman jihar Karaɗuwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban kwamitin neman ƙirƙiro jihar Karaɗua Alhaji Kabir Aliyu Maska ya cigaba da cewa suna da fafutukar neman jihar ne domin samun cigaban dukkanin al’ummomin jihohin baki ɗaya.

Maska ya bayyana haka ne a yayin da kwamitin ya kai ziyara tare da gabatar da kundin sa ga sakataren gwamnatin jihar Katsina.

Kwamitin wanda ke yaƙin neman jihar Karaɗua suna cigaba da ƙoƙari don ganin an samu kafuwar sabuwar jihar wanda suka bayyana hakan a matsayin wani babban cigaba ga dukkanin al’umma musamman na jihar Katsina.

Da yake jawabi a lokacin ziyarar, shugaban kwamitin Alhaji Kabir Aliyu Maska ya bayyana cewa, “ba gajiya da zama yan jihar Katsina bane yasa muke neman jihar Karaɗua ba sai domin samun cigaban dukkanin al’ummar jihohin baki ɗaya,”Inji shi.

Ya kuma yi godiya ga Gwamnatin jihar Katsina bisa goyon bayan da kwamitin yake samu a ko da yaushe na ganin an cimma dukkanin buƙatu.

A nashi jawabin, sakataren gwamnati Barista Abdullahi Garba Faskari yayi maraba tare da nuna goyon bayan sa ga ƙudirorin kwamitin in da shima ya bayyana hakan a matsayin wani babban cigaba da jihar Katsina za ta samu idan hakan ta yiwu.

Kwamitin tuni ya miƙa wannan buƙata ga kwamitin sauraren buƙatar ƙirƙiro sabbin jihohi na majalisar ƙasa da suka zauna a kwanakin baya a Kano.

By ukarofi