Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙaramar hukumar Funtua Abdulmutallab Suleiman Goya ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa kan ƙirƙirar cibiyar koyon sana’o’i a yankin da ya ce wannan cibiya ta sanya matasa maza da mata suna tururuwan shiga makarantar.
Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata takardar sanarwa mai ɗauke da sa hannun Bashir Yero,jami’in watsa labarai na ƙaramar hukumar Funtua.
Alhaji Goya ya yi wannan yabo ne a yayin bikin ƙaddamar da fara horaswa da kuma buɗe cibiyar koyon sana’o’in wadda wanda a cewar sa za ta taimaka wajen ba matasa maza da mata ƙarin ƙwarewa da faɗaɗa sana’o’in su domin dogaro da kai.
Sana’o’in da za a koyar a cibiyar sun haɗa da sana’ar ɗinki, ƙunshi da sarrafa sabulu, man shafawa,da gyaran gashi na maza da mata.akwai kuma koyon aikin sa wuta mai amfani da hasken rana (solar installation)Koyon girke-girke.
Sai Sana’ar yin jaka da takalma (leather work)
Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa irin waɗannan cibiyoyi a Funtua, Ɓatagarawa, Jibiya da Mai’adua kaɗai ake da su da gwamnatin Dikko Raɗɗa ya gina a jihar.
Sai ya jawa hankalin ɗaliban da su dage wajen karatu da aiwatar da dukkan darussa domin su samu ingantacciyar ƙwarewa da za ta basu damar dogaro da kawunan su.
Ya ce an samar da cibiyoyin ne ta haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin ƙasar Jamus da Centre for Community Development and Research Network (CCDRN) da kuma Gwamnatin Jihar Katsina.
Alhaji Goya ya ƙara da cewa dukkan kwasa-kwasan da ake koyarwa an wadata su da kayan aiki na zamani. Haka kuma ya yi alƙawarin ba wa ɗaliban yan asalin ƙaramar hukumar Funtua jari bayan kammala horo, tare da ci gaba da biyansu kuɗin sufuri har tsawon lokacin da za a kammala horaswar.
A nasa ɓangaren, Ko’odinetan shirin, Malam Abubakar Tukur, ya bayyana cewa horon zai ɗauki tsawon watanni shida, sannan a yaye ɗaliban, a kuma ɗauki sabon rukuni. Ya ce shirin zai ci gaba har zuwa shekaru huɗu nan gaba.
A wannan zangon dai, matasa maza da mata 130 daga mazaɓun Maska, Dukke da Makera ne suka sami damar shiga cikin shirin.
A jawaban sa Shugaban kwamitin gudanarwa na Cibiyar, Mai Unguwa Abubakar Sani ya yi godiya ga Shugaban ƙaramar hukumar Funtua da Gwamnan Jihar Katsina saboda samar da wannan muhimmiya cibiyar.
Ya bayar da tabbacin cewa za su kula da tsari da ingancin horaswar domin tabbatar da cimma burin shirin.
