Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta shiga tattaunawar diflomasiyya ta matakai mafi girma domin ganin an saki jirgin saman rundunar sojin sama ta NIjeriya, NAF C-130, da kuma sojoji 11 da gwamnatin sojin Burkina Faso ta tsare har tsawon kwana uku a jere.
Rahotanni sun nuna cewa an tsare jirgin ne bayan ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izini ba, lamarin da ya haddasa ɗaurewar girar juna tsakanin ƙasashen biyu.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar cewa batun ya wuce hannun rundunar sojin sama, yanzu kuma Ma’aikatar Harkokin Waje ce ke jagorantar tattaunawar.
Wata majiya ta soji ta shaida cewa, “Ba a sake su ba tukuna. Ma’aikatar Harkokin Waje ce yanzu ke riƙe da lamarin. Muna fatan za a warware komai nan ba da jimawa ba.”
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya kuma tabbatar da cewa ofishin jakadancin Nijeriya da ke Ouagadougou ya fara tattaunawa da hukumomin Burkina Faso domin sasanta rikicin.
A gefe guda, hukumar labarai ta gwamnati a Burkina Faso (AIB) ta ruwaito cewa an tsare jirgin ne bisa zargin karya dokar shiga sararin ƙasar ba tare da samun izinin tashi da sauka ba.
ƙungiyar Confederation of Sahel States (AES) ta yi zafi wajen sukatar abin da ta kira keta ikon mallakar ƙasa, tana mai cewa bincikenta ya gano cewa jirgin bai da izinin wucewa ta sararin Burkina Faso a lokacin da aka kama shi.
Sai dai rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta fitar da wata sabaniyar sanarwa, inda ta ce ba laifin karya dokar sararin ƙasa ba ne ya sa aka tsaida jirgin, illa kawai jirgin ya yi saukar gaggawa a Bobo-Dioulasso saboda wata matsalar fasaha da aka gano bayan tashin jirgin daga Legas a ranar 8 ga Disamba, 2025.
Kakakin NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa matukan jirgin sun bi ƙa’idojin tsaron sufurin jiragen sama na duniya wajen karkata zuwa filin sauka mafi kusa. Ya tabbatar cewa sojojin na cikin ƙoshin lafiya, kuma ana kula da su cikin mutuntawa a hannun hukumomin Burkina Faso.
Ya ƙara da cewa, ana ci gaba da tattaunawa domin warware sauran batutuwa, tare da sa ran jirgin zai ci gaba da tafiyarsa zuwa Portugal kamar yadda aka tsara tun farko.
