Yadda muhawara ta ɓarke bayan ganawar Atiku da Jonathan 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Muhawara ta ɓarke a fagen siyasar Nijeriya, bayan wata ganawa da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar, ya yi da tsohon shugaban ƙasar Good Luck Ebele Jonathan.

‘Yan siyasar biyudai basu fito fili sun yi bayanin abubuwan da suka tattauna ba, amma mutane da dama na alaƙanta ganawar ta su da shirye shiryen tunkarar zaɓen shugaban ƙasar na 2027.

Ana dai raɗe raɗin cewa dukkansu, na da sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Ganawar jiga-jigan ‘yan siyasar ta gudana ne a Abuja inda Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriyar Good Luck Jonathan har gida, duk da irin tsamar siyasar da ke akwai a tsakaninsu, duba da cewa Atikun na cikin waɗanda suka jagoranci kifar da gwamnatin Jonathan a zaɓen 2015.

Masana siyasa a Nijeriya dai na da bambancin ra’ayi akan yadda suke kallon wannan ganawa tasu.

Farfesa Abubakar Kari, masanin siyasa ne kuma malami a jami’ar Abuja, ya shaida wa BBC cewa, ba abin mamaki ba ne manyan ‘yan siyasa kamar waɗannan su haɗu su gana har ma su tattauna.

Ya ce,” Ba mamaki da yake ana danganta dukkansu da waɗanda za su tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, to kila so suke su magantu ne don su fahimci juna, wala’ala ko daya ya janyewa daya ko kuma a ƙulla wata alaƙa ko haɗaka.”

Shi kuwa a nasa ra’ayin, Dakta Yakubu Haruna Ja’e, masanin siyasa kuma malami a jami’ar Kaduna, ya shaida wa BBC cewa, ganawar za ta firgita mutane da dama a ƙasar.

Ya ce,” Ganawar za ta firgita ‘yan siyasa manya da ke son tsayawa takara, sannan kuma ita gwamnati mai ci ita ma wannan ganawa za ta firgita ta, kuma akwai yiwuwar cewa suna shirye-shiryen fitar da wanda ya kamata don su ƙwace mulki daga hannun jam’iyya mai mulki.

“Wannan zama da suka yi ba zai rasa nasaba da shawarar wanda zasu tsayar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba,” inji shi.

Wannan dai na faruwa ne yayin da wasu bayanai ke cewa tuni tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar ya fara shirin zabar wanda zai masa takarar mataimakin shugaban ƙasa, inda wasu majiyoyi ke cewa ya na tunanin ɗaukar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jama’iyyar Labour Peter Obi, ko kuma tsohon gwamnan jihar Ribas Rotimi Amaechi.

By ukarofi