Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ƙaryata wani rahoto da ke iƙirarin cewa ya ce lokaci ya yi da yankin Kudu zai fitar da Shugaban ƙasa a shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, El-Rufai ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya, yana mai cewa bai taɓa yin irin wannan furuci ba a cikin jawaban da ya gabatar, hirarraki ko kuma rubuce-rubucensa a kafafen sada zumunta.
Ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da editoci da su cika nauyin da ya rataya a wuyansu, tare da gujewa yaɗa labaran bogi.
El-Rufai, wanda mamba ne na jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC), yana ƙalubalantar sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
“An ja hankalina zuwa wani labarin bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke iƙirarin cewa na bayyana wane yanki ne ya kamata ya fitar da Shugaban ƙasa a 2027.
“Wannan iƙirari ba gaskiya ba ne, duk da yadda ya bazu. Ban taɓa yin irin wannan magana ba a cikin kowanne jawabi, hira ko rubutu a kafafen sada zumunta na. Ina da shafuka na gaskiya da ake iya tantancewa a kafafen sada zumunta inda nake bayyana ra’ayoyina kuma nake ɗaukar alhakin abin da na faɗa.
“Ina so in jaddada cewa babu wani ra’ayi da za a danganta mini sai wanda na faɗa kai tsaye a shafukana na sada zumunta ko a hirarraki da kafafen yaɗa labarai masu mutunci. Haka kuma ba daidai ba ne a danganta mini ra’ayoyin da ke cikin rubuce-rubucen wasu marubuta da na wallafa a shafukana a matsayin gudummawa ga tattaunawar ƙasa.
“Waɗannan bayanai suna da matuƙar muhimmanci yayin da muke fuskantar siyasar rashin ɗa’a da kuma amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa labaran ƙarya. Danganta mini maganganun da ban faɗa ba daga wani dandalin labaran bogi ba ya ba da hujjar ɗaukar irin waɗannan kafafe da muhimmanci.”
Tsohon gwamnan na Kaduna ya ci gaba da cewa: “A wannan zamani na rikice-rikice da ƙarya, wajabcin tantance gaskiya kafin wallafawa ya ƙara zama dole. A wannan lamari, wasu manyan editoci sun yi watsi da wannan nauyi. Al’umma na asara idan shugabannin kafafen yaɗa labarai suka haɗa kai da marasa ɗa’a a kafafen sada zumunta wajen yin gasar ƙirƙirar labaran ƙarya. Kowa ya kamata ya cika nauyin da ya rataya a wuyansa.”
