Dalilan da ya sa manyan ‘yan siyasa a jam’iyyun adawa ke dawowa APC – Fadar Shugaban ƙasa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Fadar Shugaban ƙasa ta yi watsi da iƙirarin da wasu shugabannin jam’iyyar adawa a Nijeriya ke yi cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na yi wa wanzuwar jam’iyyun siyasa barazana da amfani da yaƙi da cin hancinta wajen cimma burinta na siyasa.

‘Yan jam’iyyar adawar da suka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP, Peter Obi, da shugaban jam’iyyar ADC, David Mark; su ne suka yi wannan iƙirari a ranar Lahadi.

Sun yi zargin cewa yawan sauyin sheƙa zuwa APC na zuwa sakamakon matsin lamba da bincike-bincike da barazana ta shari’a da sauran nau’o’i na tilastawa.

Sai dai mai magana da yawun Shugaban ƙasa Bayo Onanuga, a cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce, ba wanda ake tilasta wa dawowa APC. Ya ce masu sauyin sheƙar na yin hakan ne bisa raɗin kansu saboda irin nasarorin gwamnatin Shugaba Tinubu ke samu a sauye-sauyen da take kawowa.

“Suna zargin murƙushe jam’iyyun siyasa ne saboda yadda manyan ‘yan siyasa ke dawowa jam’iyyar da ake ƙara samun farin jini ba tare da wani ya tilasta musu ba. Kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa kowa damar shiga kowacce jam’iyya wanda ya ba su damar su zaɓi inda suke so su kasance a lokacin da suke so.

“Ba wanda aka tilasta wa domin shiga APC. Duk wanda ya shigo, ya shigo ne a bisa raɗin kansa. Sun gamsu ne da irin nasarorin da gwamnatin Tinubu take samu,” inji sanarwar.

Onanuga ya ce, zargin cewa APC na yaƙin sunƙuru wata hanya ce ta janye hankalin Shugaba ƙasa ta hanyar irin waɗannan iƙirari da nufin ƙalubalantar nasarar da gwamnatin Tinubu da jam’iyyar APC ta samu a cikin shekara uku.

Wasu da ke kiran kansu ‘yan jam’iyyar adawa da suka haɗa da waɗanda suka bar jam’iyyar saboda gaza cikar burinsu na samun muƙami da nufin nemar wa kansu mafita.

A ranar Lahadi, wata ƙungiyar ‘yan adawa sun haɗu domin yin irin waƙar da suka saba yi da nufin ganin ƙoƙarinsu na sukar gwamnati.

Sun yi zargin cewa jam’iyyun siyasa na fuskantar barazana saboda manyan ‘yan siyasa na shiga jam’iyyar APC bisa raɗin kansu. Kundin tsarin mulkinmu ya ba da ‘yancin shiga ƙungiya da kuma ‘yancin shiga kowacce jam’iyya a lokacin da suke so.

Ba mutum koɗaya cikin waɗanda suka shiga APC da aka tilasta wa. Sun yanke shawarar ce bayan ganin irin cigaban da Shugaba Bola Tinubu ya kawo.

Za ka iya tambaya: Idan ‘yan siyasa suna tururuwar komawa jam’iyyar PDP a tsakanin 2000 zuwa 2015, to shin an raunata dimokuraɗiyya ne?

Haka kuma, bincike da hukumar EFCC ke yi ya fara fito da irin yadda su suka riƙe ofisoshinsu da dukiyar al’ummar da aka ba su amana. Waɗannan ‘yan siyasa ne ke zargin shugaban Tinubu da amfani da EFCC domin cimma muradan siyasa.

A yayin da fadar shugaban ƙasa ba ta da hurumi a ayyukan EFCC, lallai ne mu jaddada cewa EFCC hukuma ce mai zaman kanta da doka ta kafa da ba ta damar gudanar da ayyukanta ba tare da katsalandan ba.

Hukumar an ɗora mata alhakin bincike da gurfanar da masu laifi a gaban kotu ba tare da la’akari da waɗanda abin ya shafa ba ko alaƙarsa da wata siyasa ko matsayinsa a cikin al’umma. Muna mamakin yadda masu iƙirarin ceto Nijeriya s baya a yanzu suke yaƙar batun bincike da bin diddigi.

Duk waɗanda suke fuskantar tuhuma a gaban EFCC, kamata ya yi su je su amsa, su wanke kansu idan suna da da iko.

Shugaba Tinubu ba ya bai wa hukumar yaƙi da cin hanci umarni kan wa za su bincika ko su kama ko su gurfanar a gaban kotu.

Shugaba Tinubu yana da muhimman abubuwa da ake gabansa kuma ba shi da lokacin tattauna lamarin siyasa.

Sannan kotu ce ke hukunci kuma waɗanda ba su da laifin komai za kuɓuta.

Ba wanda ya fi ƙarfin doka. Duk wanda aya ci ladan kuturu dole ya yi masa aski. Dangantaka ta siyasa ba za ta hana EFCC gudanar da aikinta bisa doka wanda hakan ne ya taimaka wajen cire Nijeriya daga baƙin littafin jerin ƙasashen da ke safarar haramtattun kuɗi.

Muna lura kuma muna sane cewa wasu daga cikinsu da aka gudanar da bincike a kansu kuma aka gurfanar da su a gaban kotu tun kafin zuwan shugaba Tinubu a shekarar 2023.

Wasu daga cikin waɗannan ‘yan siyasar an same su da laifin safarar haramtattun kuɗi a yayin da mafi yawa daga cikin abokan harƙallarsu aka tura su gidan yarin a kasashen waje.

Muna ba ‘yan siyasar shawara ka da su ɗauki hukumomin Nijeriya ba a bakin komai ba da ƙoƙarin yaƙi da cin hanci ta amfani da siyasa domin guje wa bincike da sauransu.

Yaƙi da cin hanci haƙƙi ne da ya rataya a wuyanmu kuma bai kamata a shashantar da shi ba saboda wani zargi marar tushe ko labarin ‘yan siyasar da ke da wani gilli a zuciyarsu.

By ukarofi