Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata gobara da ta tashi da asubahin wayewar gari ta lalata aƙalla shaguna 48 a kasuwar Elegushi da ke Lekki, a jihar Legas.
Babban Sakataren na Hukumar Agajin Gaghawa ta Jihar Legas (LASEMA), Olufemi Oke-Osanyintolu, ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa, hukumar ta samu kiran gaggawa misalin ƙarfe biyu na dare, inda nan take ta tura jami’anta zuwa wurin da wutar ta riga ta kama kasuwar baki ɗaya.
A cewarsa, jami’an agajin gaggawa sun yi aiki cikin sauri tare da haɗa kai da sauran hukumomi, lamarin da ya taimaka wajen shawo kan wutar kafin ta yazu zuwa wasu gine-gine da ke makwabtaka da kasuwar.
Binciken farko da tawagar Shark Response Team ta LASEMA ta gudanar ya nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga wani rumfar wucin-gadi da ke cikin harabar kasuwar, kafin daga bisani ta bazu zuwa babban ginin kasuwar. Sai dai an bayyana cewa babu asarar rai ko rauni a sakamakon gobarar.
Oke-Osanyintolu ya ce, duk da girman asarar dukiya, an samu nasarar daƙile wutar baki ɗaya, tare da hana ta lalata wasu gine-gine da ke kusa.
Ya ƙara da cewa, tuni aka fara tantance ɓarnar da ta faru bayan gobarar, inda aka tabbatar da cewa shaguna 48 ne suka ƙone.
Ya yi kira ga ‘yan kasuwa da shugabannin kasuwanni da su riƙa ɗaukar matakan kariya daga gobara, musamman ganin yadda ake aara kusantar lokacin rani.
A cewarsa, an wayar da kan ‘yan kasuwar kan muhimmancin tanadin kayan kashe gobara, tare da shawarwarin a girka na’urorin gano hayaƙi da kararrawar gargaɗin gobara domin daƙile irin wannan iftila’i tun kafin ya yi ƙamari.
Gobara dai na ci gaba da zama ruwan dare a sassan Nijeriya, musamman a lokutan rani, lamarin da ke kara jaddada buƙatar ƙarfafa shirin kariya da kuma inganta kayan aikin masu kashe gobara a faɗin ƙasa.
