
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Kebbi ta yi bayanin haƙiƙanin abin da ya faru a Babban Asibitin Bagudo a safiyar yau Talata.
A wata sanarwa daga mai ba Gwamna Nasir Idris Shawara akan Harkar Labarai, Yahaya Sarki, gwamnatin ta ce fashewar ta faru ne sakamakon gobara ba fashewar bom ba kamar yadda aka yi tunani da fari.
Ya bayyana cewa, Sakataren Gwamnatin (SSG), Yakubu Balance Tafida ne ya faɗi haka a yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce binciken farko da rahotanni daga hukumomin tsaro sun nuna cewa fashewar mai ƙarfi ta samo asali ne daga gobara a rukunin gidajen ma’aikatan asibitin.
Ya kuma ce, gwamnatin jihar tana aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro, waɗanda tuni suka ɗauki matakai da suka dace akan al’amarin.
Ya ƙara da cewa babu asarar rai a sakamakon haka, saidai gobarar ta shafi wani gini kuma tuni mazauna wannan yankin sun fice ba tare da sun jikkata ba.
Kazalika, gwamnatin ta kirayi al’umma da su kwantar da hankali, sannan su guji yaɗa bayanai marasa tabbas da ka iya haifar da firgici, tana mai cewa dukkan hukumomin tsaro suna aiki tuƙuru wajen shawo kan al’amarin, yayin da ake cigaba da bincike don gano ainihin musabbabin tashin gobarar.
Ya kuma yaba wa rundunar ƴan sandan jihar da sauran jami’an tsaro bisa ga gaggawar ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron yankin da ma al’umma baki ɗaya.
