Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gamayyar ƙungiyoyin ma’aikatan manyan makarantun gaba da sakandare .allakar Jihar Katsina (JCF) ta fitar da sanarwar gargaɗi ga gwamnatin Jihar Katsina, bayan tattaunawa mai zurfi da ta shafi manyan batutuwan ci gaban makarantun jihar.
Sanarwar, wadda ta fitar shugaban gamayyar, Comrade Muhammad Nasir Gidado na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina Polytechnic, ta nuna takaicin ƙungiyar kan yadda gwamnati ta nuna halin ko-in-kula duk da matakan da suka bi na tattaunawa a baya.
Ƙungiyar ta ƙunshi malamai da sashen gudanarwa daga manyan makarantun jihar guda shida, da suka haɗa da kwalejin Ilimi ta Isah Kaita Dutsin-ma, Kwalejin Dr. Yusuf Bala Usman Daura, da Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Ungozoma da ke da rassan Katsina da Malumfashi, da sauran cibiyoyin ilimi na jiha.
A yayin taron da ya gudana a sakatariyar, Malaman Hassan Usman Katsina Polytechnic, JCF ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati bata ɗauki mataki cikin sati biyu ba, to za su ɗauki matakai na ƙarshe domin kare muradun ma’aikatan ilimi da cigaban cibiyoyin ilimi na jiha.
Wasu daga cikin shugabannin ƙungiyoyin da suka yi jawabi a wajen taron sun haɗa da Dakta Sabi’u Ya’u, tsohon shugaban ƙungiyar malamai ta Hassan Usman Katsina Polytechnic, da Dakta Garba Idris Yargamji, shugaban ƙungiyar malamai ta Isah Kaita College of Education.
