Gwamnatin Katsina ta karɓi mabarata 11 da aka maido daga Abuja

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan raya Karkara da kyautata rayuwar al’umma Farfesa Abdulhamid Ahmed ne ya karɓi mutanen a hannun wakilan hukumomin Abuja da suka maido su, a madadin Gwamnatin Jihar Katsina.

An dai maido mutanen ne a ƙarƙashin Shirin tsaftace birnin tarayya Abuja mai suna “Operation Sweep Abuja” wanda ministan Abuja Nyesom Wike ya ƙirƙiro da shi.

Mutanen su 11 sun ƙunshi maza biyar sai mata su shida, kuma daga cikin su akwai ƙananan yara ya’yan wasu daga cikin matan.

Da yake jawabi a lokacin da yake karɓar mutanen, Farfesa Abdulhamid Ahmed ya ce, waɗanda aka maido yan asalin ƙananan hukumomin Katsina, Daura, Safana da kuma ƙaramar gukumar Ƙanƙara.

Farfesa Abdulhamid Ahmed wanda Daraktan Walwalar Jama’a Alhaji Jibrin Mukhtar ya wakilta ya ce, ma’aikatar za ta miƙa mutanen ga iyalan su.

A cewar shi, wannan shi ne karo na 4 da hukumomin Birnin Tarayya Abuja suka maido da yan asalin jihar da ke barace-barace da kwana a gidajen da ba’a kammala gina su ba a Abuja.

Farfesa Abdulhamid Ahmed ya buƙaci yan asalin Jihar Katsina akan su ƙauracewa zuwa Birnin Abuja domin yin barace-barace.

Daga nan sai ya bada tabbacin cewa, kafin miƙa mutanen ga iyalan su, za’a basu shawarwari domin gyaran aƙidar su.

Wasu daga cikin mutanen da aka maido din sun yabawa Gwamnatin Jihar Katsina akan yadda ta kula da su bayan maido su.

Sun kuma bada tabbacin cewa zasu yi kyakkyawan amfani da shawarawarin da aka basu na gyaran rayuwar su.

By ukarofi