Daga MUKHTAR YAKUBU
Masu magana su kan ce rana ba ta karya, sai dai uwar ‘ya ta ji kunya. Kamar yau ne ake ta maganar an saka ranar auren marubuci Zubairu Musa Balannaje. Cikin hukuncin Allah sai ga shi kuma har ranar ta zo.
Domin kuma a ranar Lahadi 28 ga Disamba 2025 ne aka ɗaura auren Zubairu Musa Balannaje da amaryasa A’isha Auwal Umar.
An ɗaura auren ne da misalin ƙarfe 10 na safe a masallacin Juma’a na Ammar Ibn Yassir dake Unguwar Samegu Gangar ruwa a cikin garin Kano inda ɗumbun jama’a suka taru domin shaida ɗaurin auren.
Tun kafin ranar ɗaurin auren dai uwar ɗakin marubucin Hajiya Umma Sulaiman ‘Yan Awaki ta shirya wa amarya da ango shagalin biki a ranar Juma’a 26 ga Disamba a Unguwar Rijiyar Zaki.
An dai fara shagalin bikin da misalin ƙarfe 7 na dare zuwa ƙarfe 10, kuma an yi shagali an yi Dinner.
Marubuci El-Amen Daurawa shi ne ya jagoranci taron yayin da Hadiza Maikano ta gabatar da waƙoƙinta a wajen ‘yan fim da dama ne da marubuta suka halarci taron. Daga cikin ‘yan fim ɗin da suka halarci taron akwai Hindatu Bashir, Safiya Kishiya, Yakubu Furodusa.
A ɓangaren marubuta kuwa akwai Ado Ahmad Gidan Dabino MON, Zaharddin I Kallah, Kabiru Yusuf Anka, Ibrahim Muhammad Imdabawa Adamu Yusuf Indabo, Ayuba Danzaki, Yassir I Kallah.
Sai ɓangaren mata akwai Fa’iziyya D Sulaiman, Lubabatu Ya’u Babura, Hadiza Nuhu Gudaji, Bilkisu Yusuf Ali, Amina Yusuf Ali, Bishira Nakura, Zainab Lawan Brigade, Hassana Labaran ɗanlarabawa, Jamila Abdullahi Rijiyar lemo da sauransu.
An dai yi biki an gama lafiya. Da fatan Allah ya bada zaman lafiya da ƙaruwar arziki.
