Matakin da Majalisar Dattawa ta ɗauka na sanya hukuncin kisa ga masu satar mutane a ƙarƙashin ƙudurin gyaran dokar hana ta’addanci (Terrorism Preɓention and Prohibition Act) wata babbar alama ce ta ɗaukar mataki mai ƙarfi wajen yaƙi da matsalar tsaro a Nijeriya. Duk da cewa ƙudurin ya fuskanci adawa daga ƙungiyoyin kare haƙƙin zan Adam da masana shari’a, waɗanda ke cewa hukuncin kisa ba zai hana aikata laifi ba kuma ba zai ƙarfafa tsaron ƙasa ba, to a zahiri, buƙatar ɗaukar wannan mataki ya zama wajibi kuma ba za a iya kaucewa ba.
An bayyana wannan adawa ne a wani taron jin ra’ayin jama’a da kwamitocin haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa kan shari’a, haƙƙin ɗan Adam, tsaro da harkokin cikin gida suka shirya. ƙudurin na neman ayyana satar mutane, garkuwa da mutane da makamantansu a matsayin ayyukan ta’addanci, tare da sanya hukuncin kisa ba tare da wata damar tara ko sauya hukunci ba.
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), tare da ƙungiyoyi da dama kamar ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA), Hukumar Kare Haƙƙin ɗan Adam ta ƙasa (NHRC), da sauran hukumomi, sun nuna damuwa kan ɓangarorin doka, Kundin Tsarin Mulki da manufofi. Fagbemi ya buƙaci ‘yan majalisa da su cire sashen hukuncin kisa, yana mai cewa ko da yake gwamnati na goyon bayan yaƙi da ta’addanci, wannan hukunci na iya zama abin haɗari. Ya bayyana cewa hukuncin kisa na iya bai wa ‘yan ta’adda damar ɗaukar kansu a matsayin shahidai, wanda hakan zai ƙara musu ƙarfi da jawo sabbin mabiyansu.
Haka kuma, ya gargaɗi cewa wannan hukunci na iya hana ƙasashen waje miƙa waɗanda ake zargi da aikata laifin, saboda ƙasashe da dama ba sa amincewa da hukuncin kisa. Wannan, a cewarsa, na iya sanya Nijeriya ta zama ƙasa da ke haifar da mafakar masu aikata laifi a ƙasashen waje.
Ministan ya ƙara da cewa, Nijeriya ta daɗe ba ta aiwatar da hukuncin kisa ba, abin da ya haifar da cunkoso a gidajen gyaran hali da kuma yiwuwar takurar wasu fursunoni. A ganinsa, abin da ya fi dacewa shi ne tabbatar da kama masu laifi da hukunta su yadda ya dace, maimakon tsananin hukunci. Ya ba da shawarar ɗaurin rai da rai ba tare da yafewa ba a matsayin madadin hukuncin kisa.
Hukumar NHRC ta buƙaci duk wata doka ta riƙa wucewa ta hanyar tantance tasirin ta kan haƙƙin ɗan Adam kafin amincewa da ita. Ta ce ƙudurin, ko da yake an yi shi da niyya mai kyau, na ɗauke da matsaloli masu tsanani na shari’a da kundin tsarin mulki, kuma dole ne ya dace da ƙa’idojin kare haƙƙin ɗan Adam na duniya. Ta gargaɗi cewa ƙara yawan hukuncin kisa a tsarin shari’a mai rauni na iya haifar da yanke hukunci na kuskure wanda ba za a iya gyarawa ba.
ƙungiyar NBA ta ba da shawarar a riƙa la’akari da nauyin laifi kafin yanke hukunci, ta yadda hukunci zai bambanta da tsananin laifin. Ta buƙaci a taƙaita ayyana satar mutane a matsayin ta’addanci ga lokutan da laifin ya shafi ƙungiyoyin ta’addanci ko niyyar tsoratar da jama’a ko tilasta wa gwamnati wani abu. Haka kuma, ta nemi a maye gurbin hukuncin kisa na dole da hukunci mai sassauci kamar ɗaurin rai da rai, sai a lokuta masu tsanani a yi la’akari da kisa.
Sanata Ekong Sampson ya goyi bayan wannan tsari na bambance hukunci, yana mai cewa dole ne doka ta riƙa la’akari da irin ɓarnar da aka yi, rawar da kowane mai laifi ya taka da sakamakon laifin.
Tsohon wakilin Majalisar ɗinkin Duniya kan haƙƙin ɗan Adam, Farfesa Uchenna Emelonye, ya yaba da haɗuwar ra’ayoyin manyan hukumomin shari’a wajen adawa da hukuncin kisa. Ya ce shaidu na kimiyya da ƙwarewar duniya sun nuna cewa ƙara hukuncin kisa ba zai daƙile satar mutane ba. A ganinsa, abin da Nijeriya ke buƙata shi ne gyaran hukumomi, inganta aikin ‘yan sanda, tattara bayanan sirri, tsaron iyaka da tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa.
Duk da wannan muhawara, gwamnatin tarayya ta ɗauki wani muhimmin mataki ta hanyar ayyana masu garkuwa da mutane da ƙungiyoyin ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda a hukumance. Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya sanar da hakan a taron ƙarshen shekara, yana mai cewa daga yanzu duk wanda ya tsoratar da al’umma ta hanyar satar mutane ko kai hari ga manoma, za a ɗauke shi a matsayin ɗan ta’adda.
Jaridar Blueprint na amincewa da damuwar da masu ruwa da tsaki a fannin shari’a suka nuna, domin hujjojin su na da tushe kuma suna da muhimmanci. Amma tambayar ita ce: wacce hanya ce ta fi dacewa wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan tsawon kusan shekaru ashirin ba tare da samun mafita ba?
A bisa wannan yanayi, muna goyon bayan ayyana masu garkuwa da mutane a matsayin ’yan ta’adda, tare da kira ga Majalisar Dokoki da ta gaggauta amincewa da ƙudurin gyaran dokar hana ta’addanci da zai kafa hukuncin kisa kan satar mutane. Idan hali ya tsananta, dole ne a ɗauki mataki mai tsauri domin kare rayuka da martabar al’ummar Nijeriya.
