
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce matakin ɗansa, Abba Atiku Abubakar na koma wa jam’iyyar APC mai mulki mataki ne na raɗin kansa.
A wani rubutu ta shafinsa na X, Atiku ya ce a tsarin dimukraɗiyya irin waɗannan lamuran ba sabon abu ba ne, ko da kuwa siyasa ta haɗu da alaƙar iyali.
Ya ce, “A matsayina na ɗan dimukraɗiyya, ba na tilasta wa ’ya’yan na ra’ayi a kan abubuwa da suka shafi irin wannan lamarin haka kuma bazan tilasta wa ’yan Najeriya ba.”
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada cewa ra’ayin ɗansa ba zai sa shi canza manufarsa wajen aiki domin kawo ingantacciyar shugabanci ba.
Abba Atiku dai ya sanar da barinsa PDP zuwa APC a ranar Alhamis, yayin wata ziyara da ya kai ofishin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ƙasa, Sanata Barau Jibril.
A jawabin nasa, Abba ya bayyana cewa dalilin sauya sheƙarsa shi ne sha’awarsa ga salon shugabanci da jajircewar Sanata Barau akan al’amuran siyasa da al’umma.
Ya ƙara da cewa, zai yi aiki tare da Sanata Barau domin ganin an sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
