Filato: ‘Yan bindiga sun halaka mutum bakwai a wajen haƙar ma’adinai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An tabbatar da rasuwar mutane guda bakwai sakamakon wani mummunan hari da dare a wani haramtacce wajen haƙar ma’adinai da ke yankin Kuru a Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu da ke Jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa, an kai farmakin ne da misalin ƙarfe 1 na daren Alhamis a lokacin da wasu ‘yan bindiga suke je wajen da nufin sace haramtattun kayan ma’adinai.

Mazauna yankin sun sanar da jami’an sojoji na shiyya ta 6 da ke ƙarƙashin atisayen Safe Haven (OPSH) da misalin ƙarfe 8:40 na safe, inda nan da nan aka baza dakaru zuwa wajen domin kwantar da hankalin jama’a.

Wani babban jami’in soja ya shaida wa manema labarai cewa dakarun sun samo alburusai 10 na 7.62mm a wajen da al’amarin ya faru yayin bincikensu.

Tuni aka garzaya da gawarwakin mamatan zuwa Asibitin Primary Health Care da ke Dabwak a yankin domin ba iyalansu damar shirya jana’izarsu.

Bincike ya nuna cewa waɗanda harin ya rusa da su sun kasance suna aikin ne ta haramtattun hanyoyi, wanda ya saɓa wa dokar haramcin haka da gwamnatin jihar ta yi a baya.

By Babaji