
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar APC ta yi watsi da raɗe-raɗin da ke yawo game da yiwuwar sauya Maitaimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a matsayin abokin tafiyar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
APC ta ce, zarge-zargen ba gaskiya ba ne domin ababen ne da aka ƙirƙira marasa asali da nufin ruɗar da jama’ar ƙasa.
A kwanan nan ne aka yi ta yaɗa jita-jitar cewa an zayyano sunayen wasu Kiristocin Arewa su uku da ake ganin ɗayansu ka iya maye gurbin Shettima a muƙamin domin mayar da tikitin APC ya zama ‘Muslim – Christian’ a zaɓen 2027, a wani mataki na samar da daidaito a shugabanci.
Mutanen sune: Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara; Bishop Matthew Hassan Kukah; da kuma Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa Gwabin.
A wata sanarwa da APC ta fitar a ranar Litinin ta hannun Sakatarenta na ƙasa, Felix Morka, ta kirayi gidajen jaridu da su ƙaurace wa bada aron kafafensu ga masu ƙoƙarin yaɗa jita-jitar da ba ta da makama, wadda ake yaɗawa da nufin haddasa ruɗani acikin jama’a.
Ya bayyana cewa, a yanzu dokar APC ta haramta dukkan wasu ayyuka da suka shafi siyasa, a madadin haka suna aiki tuƙuru wajen mara wa Shugaba Tinubu da Shettima baya wajen sauke nauyin gwamnati na Ajandar Sabunta Fata da ƙoƙarin aiwatar da gyare-gyaren al’amuran tattali da aka samar domin ciyar da Nijeriya da al’ummarta gaba.
A ƙarshe, jam’iyyar ta kirayi ministoci, manyan jami’an gwamnati da jami’an jam’iyya da su guji yin tsokaci akan jita-jitar da ba ta amfani da mayar da hankali akan ayyukansu ga gwamnati da jam’iyyar gami da ƙoƙarin ƙarfafa wa nasarorin Shugaba Tinubu.
