Tinubu ya zame yayin bikin marabtarsa a Turkiyya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Talata ne Shugaba Bola Tinubu ya yi tuntube ya zame a yayin wani bikin na masa maraba da zuwa a Ankara, babban birnin Turkiyya.

Lamarin ya faru ne a lokacin da shugaban Nijeriyar ke tafiya tare da Shugaba Recep Tayyip Erdoğan na ƙasar a wurin taron, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Wani gajeren bidiyo a kafar X ya nuna yadda al’amarin ya faru wanda ya haddasa cece-kuce musamman ganin yadda aka hango Shugaba Tinubu ya kusa faɗuwa yayin da suke tsakar tafiya da Shugaba Erdogan.

To saidai kuma mai ba wa shugaban ƙasa shawara akan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu bai ji rauni ba bayan tuntuɓe da ya yi har ya faɗi ƙasa a yayin taron.

“Wani bidiyo da aka wallafa a shafin X na shugaban Turkiyya ya nuna yadda kafet ya sanya Tinubu tuntuɓe kafin a yi gaggawar kai masa ɗauki”, kamar yadda BBCHausa ta wallafa.

By Babaji