Duk magoya bayana su bi Gwamnan Kano Abba – Sanata Barau Maliya

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Mataimakin shugaban Majalisar Dattijai ta Nijeriya Sanata Barau I Jibrin ya yi kira ga duk magoya bayansa su goyi bayan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2027.

Sanata Barau wanda shi ne ke wakiltar mazaɓar Kano ta Arewa a majalisar dattijan Nijeriya ya bayyana haka ne a ranar Litinin, yayin da yake jawabi a gidan gwamnatin Kano, lokacin da Gwamna Abba ya shiga jam’iyyar APC.

Kalaman ɗan majlisar, wanda ya yi amfani da kalmar 4+4, ma’ana yin gwamna wa’adi biyu, na nufin cewa ya jingine buƙatarsa ta takarar gwamna a zaɓe mai zuwa.

Barau Maliya ya tabbatar da cewa tunda dai Gwamna Abba ya riga ya shigo APC ya ce babu shi ba takara yana mai cewa duk wata gudunmawa za su bashi domin ya kai ga ci.

BlueprintManhaja ta ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma APC ne ranar Litinin da ta gabata, lamarin da ya sauya siyasar jihar Kano a daidai wannan lokaci.

By ukarofi