*Ji nake kamar a mafarki – Kwankwaso
*Kwamishinoni biyar da hadiman gwamnatin Kano 10 sun yi tutsu
*Za mu kawo ƙarshen rikicin masarautar Kano – Gwamnatin jiha
*Har yanzu ’yan uwa muke da Kwankwaso – Ganduje ya buɗe ƙofar sulhu
*Gwamnatin Kano ta shawarci mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam ya ajiye aiki
Daga NAISR S. GWANGWAZO A Abuja, IBRAHIM HAMISU a Kano da MAHDI MUSA MUHAMMAD a Kaduna
Dambarwar siyasa a jihar Kano ba baƙuwar abu ba ce, sai dai kuma a wannan karon ta faru a wajen da ba a yi zato ba, inda siyasar Kwankwasiyya da faɗa kwamacala sakamakon rabewa da aka samu tsakanin jagoran tafiyar, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da ɗan gidansa a siyasa kuma gwamnan jihar, Injinya Abba Kabir Yusuf. Wakilan Blueprint Manhaja sun tattaro yadda dambarwar take afkuwa.
Ji nake kamar a mafarki – Kwankwaso
Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam’iyyar NNPP a Nijeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, ji yake yi kamar a mafarki abin da yake faruwa a siyasar Kwankwasiyya yake afku sakamakon barin sa da na hannun damansa kuma gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi, yana mai ƙara cewa, yana da yaƙinin cewa sai Gwamna Abba Kabir da muƙarrabansa sun yi da-na-sanin fita daga jam’iyyar NNPP da suka yi.
Sanata Kwankwaso ya ce, fitar gwamna Abba daga jam’iyyar NNPP ta zo da ba-zata ga mutane da dama, kuma shi da kansa jin abin yake kamar a mafarki.
”Da yawa mutane Ina da labarin, gani suke ma kamar wani tsari ne, da ni da shi, ko da ni da su. Ni ma sau da yawa ba na yarda cewar abubuwan da suke faruwa haka su ke,” in ji Kwankwaso a tattaunawarsa da BBC Hausa.
A ranar Litinin 26 ga Janairu, 2026 gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya koma APC a hukumance, bayan sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar Juma’a 23 ga Janairu, 2026, ƙasa da shekara uku bayan cin zaɓen gwamnan Kano a cikinta.
Kwamishinoni biyar da hadiman gwamnatin Kano 10 sun ajiye muƙaminsu
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Aƙalla kwamishinoni biyar da kuma hadiman gwamnati 10 ne suka yi murabus daga muƙamansu tare da ayyana biyayya da goyon baya ga jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso biyo bayan ficewar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Rahotanni sun nuna cewa, murabus ɗin ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar tashin hankalin siyasa da rabuwar kai tsakanin Kwankwaso da Abba.
Daga cikin kwamishinonin da suka yi murabus akwai Kwamishinan Matasa da Wasanni kuma ɗan Kwankwaso, wato Mustapha Rabi’u Kwankwaso; Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dr. Yusuf Ibrahim ƙofar Mata; Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Nasiru Sule Garo; Kwamishinan Jinƙai, Adamu Aliyu Kibiya, da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, AVM Ibrahim Umar (mai ritaya).
Kazalika, sauran manyan jami’an da suka yi murabus sun haɗa da Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano, Laminu Rabi’u ɗanbaffa; Shugaban Gidan Zoo na Kano, Sadiƙ Kura Muhammad; Shugaban Hukumar KARMA, Alhaji Hassan ɗanbappa, da Sani Shehu Makarya (Igwe China), mai bai wa gwamna shawara kan kasuwar GSM.
Haka kuma, a jerin akwai Walidin Kwankwasiyya, Mai Taimaka wa Gwamna kan harkokin Masarautu; Hajiya A’in Jafaru Fagge, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Yaɗa Kyakkyawan Saƙo; Mujtaba Muhammad Auwal, Jami’in Alhazai na ƙaramar Hukumar Gwale; Hon. Nafiu Umar ɗankura, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan ƙa’idoji (SSA Protocol) a Abuja; Aminu Sa’idu, Meenan Kwankwasiyya, da Shafa’atu Ahmed LondonBe.
A cikin bayanan murabus ɗinsu, jami’an sun bayyana cewa, sauye-sauyen siyasa da rikicin cikin gida a jihar Kano ne suka sa suka ɗauki wannan mataki tare da tabbatar da ci gaba da mara wa tafiyar Kwankwasiyya da jagoranta, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, baya.
Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma jam’iyyar APC a hukumance a ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026.
Za mu kawo ƙarshen rikicin masarautar Kano – Gwamnatin jiha
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta ce nan ba jimawa ba za ta kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana faruwa kan masarautar Kano, inda mutum biyu ke iƙirarin kasancewa halastattun sarakuna.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’amuran Cikin Gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ya ce gwamnati ta tsara abubuwa na musamman domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan sarautar.
Kusan shekaru biyu kenan Kano na fama da rikicin sarauta, inda Sarki Muhammadu Sanusi II ke zaune a fadar Gidan Rumfa, yayin da Sarki Aminu Ado Bayero ke zaune a fadar Nassarawa ƙarƙashin tsaron jami’an gwamnatin tarayya.
Yayin da yake jawabi a wani shirin na musamman a gidan rediyon Muhasa da ke Kano, Waiya ya ce sauyin shekar Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC a wannan makon ce za ta kawo maslaha daga matsalar.
“Ina tabbatar muku cewa nan ba da jimawa ba, gwamnatin Kano za ta warware rikicin sarautar Kano, domin yanzu mun zama ɗaya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa masu da’awar sarautar da kansu na iya taka rawa wajen warware rikicin, inda ya ce: “Mai yiwuwa wani ya sauka daga kujerar sarauta da kansa, ko kuma wasu su nemi sulhu saboda a samu jituwa.”
Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin jihar ta kuduri aniyar tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki, tare da tabbatar da cewa ba a bari lamarin ya haifar da tashin hankali ko ya kawo cikas ga mulkin jihar ba.
“Hanyar da muke bi tana kan girmama doka, sarautun gargajiya, da kuma muradun jama’ar jihar Kano,” inji shi.
Kan sauyin jam’iyyar gwamna zuwa APC, Waiya ya bayyana matakin a matsayin ci gaban da zai kawo gagarumin alheri ga jihar.
Har yanzu ’yan uwa muke da Kwankwaso – Ganduje ya buɗe ƙofar sulhu
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana shirinsa na sulhu da tsohon abokin siyasarsa kuma abokin hamayyarsa na tsawon lokaci, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, alamar da ke nuna yiwuwar kawo ƙarshen dogon rikicin siyasa a Jihar Kano.
Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wata hira da BBC Hausa a ranar Laraba, inda ya ce sauye-sauyen siyasa da ke faruwa a jihar sun samar da damar hadin kai da fahimtar juna tsakanin manyan jiga-jigan siyasa.
Ya ce yana da kyakkyawan fata cewa nan gaba kaɗan za a samu sulhu tsakaninsa da Kwankwaso domin su ci gaba da tafiya tare kamar yadda suka taɓa yi a baya.
“Da yardar Allah muna fatan nan ba da jimawa ba za mu sasanta da Kwankwaso domin mu ci gaba tare. Mun taɓa kasancewa a sansanin siyasa guda, kuma har yanzu mu ’yan uwa ne,” inji Ganduje.
Tsohon gwamnan na Kano ya jaddada cewa abin da ya fi ba shi muhimmanci a yanzu shi ne cigaba da kwanciyar hankali a Kano, tare da tabbatar da nasarar jam’iyyarsa ta APC, maimakon ci gaba da riƙe rikice-rikicen siyasa da ka iya kawo cikas ga tafiyar gwamnati.
Ya bayyana cewa, sabon tsarin siyasar da ke kunno kai a Kano ya rage zafin adawa da rarrabuwar kawuna da aka saba gani a baya, yana mai cewa haɗin kan shugabanni shi ne ginshiƙin samar da ingantacciyar gwamnati.
“A halin da ake ciki yanzu, siyasar gaba da juna ta ragu sosai a Kano. Hankalinmu yana kan yadda za a samar wa al’umma kyakkyawan shugabanci,” inji shi.
Ganduje ya kuma yi nuni da cewa nasarar gwamnati a Kano ya kamata a ɗauke ta a matsayin nasara ta kowa da kowa, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.
“Idan Abba ya yi nasara, dukkanmu mun yi nasara ne. Idan kuma muka yi nasara, shi ma ya yi. Wannan fahimta ce ya kamata mu runguma domin gwamnati ta ci gaba da tafiya yadda ya kamata,” ya ƙara da cewa.
Har ila yau, Ganduje ya bayyana cewa gogewarsa a matsayin shugaban jam’iyya a matakin ƙasa ta ba shi ƙarin fahimta kan yadda ake warware rikice-rikice, tafiyar da dimokuraɗiyya a cikin jam’iyya, da kuma muhimmancin haɗin kai wajen tabbatar da daidaiton siyasa.
Yayin da aka tambaye shi game da makomar siyasar Gwamna Abba Kabir Yusuf a cikin APC, Ganduje ya ce yana tafiya ne bisa tsarin jam’iyya da al’adunta.
“Na san yadda jam’iyya ke aiki. Akwai dokoki, akwai kuma al’adu. Daga cikin al’adun jam’iyyar akwai bai wa gwamna mai ci damar farko, amma wannan bai shafi sauran muƙamai ba,” inji Ganduje.
Maganganun na Ganduje na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da hasashen yiwuwar sauye-sauyen siyasa a Kano, lamarin da ka iya sauya fasalin siyasar jihar gabanin zabuka masu zuwa.
Gwamnatin Kano ta shawarci Mataimakin Gwamna, Aminu Abdussalam ya ajiye aiki
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa, zai fi dacewa Mataimakin Gwamnan Jihar, Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi murabus daga muƙaminsa idan ba zai iya bin tafarkin siyasa ɗaya da Gwamna Abba Kabir Yusuf ba. Waiya ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a gidajen rediyo a Kano. Kwamishinan ya ce, rashin jituwa a ƙolin gwamnati na iya kawo rashin amincewa da tasirin shugabanci, musamman ma saboda rawar da Mataimakin Gwamna ke takawa a tsarin mulki.
Kazalika Waiya ya ce, idan manyan jami’ai sun ci gaba da bin hanyoyi daban-daban na siyasa, hakan na iya jawo rashin hadin kai a gwamnati.
Ya ƙara da cewa, duk da cewa sha’awar siyasa abu ne na al’ada a Kano, idan ra’ayin mutum ya saba da manufar gwamnati, hanya mafi daraja ita ce ya fice daga ofis don ci gaba da burinsa a fili.
Waiya ya jaddada cewa gwamnati na mai da hankali ne kan manufofin “Kano Farko,” inda ya ce ci gaban jihar ya fi muhimmanci fiye da kishin jam’iyya ko son kai.
