Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sarkin Gwandu na 19 kuma dogarin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Mustapha Jokolo, ya yi kakkausar suka ga manyan shugabannin Arewa, yana mai kira da a daina ɗora wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu alhakin matsalolin da ke addabar Nijeriya, maimakon haka a fuskanci gazawar shugabancin yankin tsawon shekaru.
A wani bidiyo da aka gani, Jokolo ya bayyana cewa durƙushewar ci gaban Arewa ba za a raba ta da halayen wasu daga cikin manyan shugabannin yankin ba, duk da cewa Arewa ta jima tana riƙe manyan muƙaman siyasa da soja tun bayan samun ’yancin kai.
A cewarsa, yankin ya samar da shugabannin ƙasa da dama, ministoci masu muhimmanci musamman a ɓangaren man fetur, da kuma manyan hafsoshin soja, amma duk da haka ba a ga gagarumin ci gaba da ya dace da wannan dogon tasiri ba. Ya danganta hakan da son kai, rashin ƙwarewa da kuma shugabanci mai fifita ’yan tsiraru.
Jokolo ya yi tsokaci kai tsaye kan mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya bayyana shekaru takwas ɗin a matsayin wata dama da ta salwanta ga Arewa.
Ya yi zargin cewa Buhari ya bari wasu tsirarun mutane masu tasiri sun mamaye harkokin tafiyar da mulki, yana ambaton Mamman Daura a matsayin ɗaya daga cikin irin waɗannan mutane, tare da cewa da’irar ta kusa da shi ba ta da faɗin gogewar da ake buƙata wajen tafiyar da ƙasa mai sarƙaƙiya irin Nijeriya.
Ya ce abin takaici ne yadda waɗannan shekaru ba su haifar da gagarumin sauyi ga Arewa ba, inda ya ce talauci, rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki suka ƙara muni a lokacin.
Yayin da yake magana kan gwamnatin yanzu, Jokolo ya kare Shugaba Tinubu, yana mai cewa yawancin matsalolin Nijeriya sun daɗe kafin hawansa mulki. Ya tuna da lokacin da Tinubu ke gwamnan Jihar Legas a zamanin Shugaba Olusegun Obasanjo, lokacin da gwamnatin tarayya ta dakatar da rabon kuɗaɗe ga Legas, amma duk da haka jihar ta ƙirƙiro hanyoyin gyara tattalin arziki da inganta harkokin kuɗi.
“Me ya sa za a ɗora wa Tinubu laifi kan komai a yau?” inji Jokolo, yana mai cewa ya kamata Arewa ta duba kanta, domin yawancin ƙalubalen da yankin ke fuskanta sakamakon matakai ne da shugabanninta suka ɗauka tsawon shekaru.
Ya kuma nuna damuwa kan abin da ya kira raunana manyan cibiyoyin Arewa. A cewarsa, hukumomin addini da na gargajiya da a baya suke ba da jagoranci na tarbiyya da zamantakewa, irin su Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci da Jama’atu Nasril Islam, sun rasa ƙarfinsu, yayin da rikice-rikicen sarauta a wasu wurare, ciki har da Kano, ke nuna rashin haɗin kai.
Dangane da rabon dukiya, Jokolo ya soki manyan attajiran Arewa bisa gazawarsu wajen zuba jari mai ma’ana a fannin ilimi da walwalar jama’a, yana kwatanta hakan da ayyukan taimako da wasu fitattun mutane daga wasu yankuna ke yi.
Ya yi kira da a koma ga ɗabi’u irin na Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello, musamman a ɓangarorin gaskiya, ɗa’a da shugabanci mai haɗa kowa. Ya yi tir da al’adar naɗa mutane a manyan muƙamai bisa kusanci maimakon ƙwarewa, yana gargaɗin cewa hakan na raunana hukumomi da daƙile ci gaba.
A ƙarshe, Alhaji Jokolo ya ce, a halin yanzu Arewa na fama da rashin daidaito da rashin alƙibla guda ɗaya. Ya jaddada cewa idan ana son ci gaba na gaskiya, dole ne yankin ya fara yi wa kansa tambayoyi masu zurfi, domin a cewarsa, “Tinubu ba shi ne babbar matsalarmu ba — mu ne matsalarmu.”
