Zargin juyin mulki: Manyan shugabannin Nijeriya da aka shirya kamawa ko kashewa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHƙ) ta tabbatar da cewa binciken da aka kammala kan wasu jami’an soji ya gano zarge-zargen shirin kifar da gwamnatin farar hula, lamarin da ya sake tayar da muhawara kan tsaron dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Bayanin ya biyo bayan rahotannin da suka daɗe suna yawo cewa wasu jami’ai sun riƙa gudanar da taruka a asirce domin tsara yadda za a hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cewar DHƙ, binciken da aka gudanar bisa ƙa’idojin soja ya gano cewa wasu daga cikin jami’an da aka kama tun a bara na da tambayoyin da za su amsa dangane da zargin shiga wani shiri da ya saɓa da rantsuwar aikinsu da kuma mutunta ikon mulkin farar hula. An ce rahoton binciken yanzu haka yana hannun manyan hukumomin soja domin ɗaukar mataki na gaba bisa dokokin rundunar soji.

Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai sun ce waɗanda ake zargin sun tsara kamawa ko kuma hallaka wasu manyan shugabannin siyasa da na soja domin samun cikakken iko cikin gaggawa. Sai dai rundunar soji ta jaddada cewa duk matakan da ake ɗauka a yanzu na cikin tsarin ladabtarwa ne, tare da tabbatar da adalci da bin doka a duk matakai.

Daga cikin sunayen da aka ambata a rahotannin kafafen yaɗa labarai akwai Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas.

Haka kuma an ambaci wasu manyan hafsoshin soji da cewa suna cikin jerin waɗanda ake shirin kama su domin hana su daƙile yunƙurin juyin mulkin. Sai dai hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan waɗannan sunaye ba a hukumance, illa dai sun ce duk wanda bincike ya nuna yana da laifi zai fuskanci kotun soja.

Sabon Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya bayyana cewa za a gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a cikin lamarin gaban kwamitocin shari’ar soja bisa tanadin dokar rundunar soji.

Ya ce wannan mataki na nufin kare martabar rundunar, tabbatar da ladabi da kuma nuna cewa sojojin Nijeriya na nan daram wajen kare kundin tsarin mulki.

Masana harkokin tsaro na ganin wannan lamari na nuna muhimmancin sa ido da tsaftace harkokin cikin gida a rundunar soji, musamman domin tabbatar da cewa dimokuraɗiyya ta ci gaba da ɗorewa ba tare da katsalandan ba. Sun kuma yi gargaɗin cewa yawaitar jita-jita kan yunƙurin juyin mulki na iya tayar da hankalin jama’a, don haka ya zama dole hukumomi su riƙa fitar da sahihan bayanai domin kawar da ruɗani.

A gefe guda, gwamnati na ci gaba da jaddada cewa hukumomin tsaro na aiki kafaɗa da kafaɗa domin kare zaman lafiya da tsarin mulkin Nijeriya, tare da tabbatar da cewa duk wani yunƙuri da ya saɓawa doka zai fuskanci hukunci mai tsauri.

By ukarofi