Amurka ta tura wa Nijeriya sojoji 200 don yaƙar ta’addanci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimanin sojoji guda 200 ne Amurka ta tura wa Nijeriya domin su bayar da horo ga dakarun tsaron Nijeriya wajen yaƙar ‘yan ta’adda, kamar yadda wani rahoto da The Wall Street Journal ta wallafa ya nuna a ranar Talata.

Wani sojan Amurka ya shaida wa jaridar cewa Amurka ta ɗauki matakin ne makonni kaɗan da Shugaba Donald Trump ya zargi Nijeriya da gaza ba al’ummar Kirista kariya daga hare-haren ‘yan ta’adda.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, ana sa ran dakarun Amurkan za su tallafa wa ayyukan yaƙi da ta’addanci ta bada horo da kuma tallafi a lamuran gudanarwa.

Ya ƙara da cewa, waɗannan sababbin sojojin da aka tura, za su tallafa wa ayyukan mashawartan sojojin Amurka da tuni suke Nijeriya wajen taimaka wa dakaru akan lamuran leƙen asiri domin gano haƙiƙanin wuraren ‘yan ta’adda da ake kai wa farmaki.

Da yake magana a ranar Talatar da ta gabata, Kwamandan tsaron Amurka reshen Nahiyar Afirka, Janar Dagvin R. Anderson, ya tabbatar da samuwar ƙarin haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin ƙasashen biyu akan muhimman al’amuran da suka shafe su.

Ya bayyana cewa, ya samu ganawa da Shugaba Bola Tinubu, inda suka tattauna tare da ƙulla yarjejeniyar buƙatar yin aiki tare domin ciyar da harkar tsaron shiyyar yammacin Afirka gaba.

By Babaji