Daga USMAN KAROFI a Abuja
A ranar Alhamis, Mai shari’a Obiora Egwuatu ya janye kansa daga shari’o’i biyu da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta shigar a kan tsohon babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami. Mai shari’ar ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne saboda dalilai na ƙashin kai da kuma domin tabbatar da adalci ya samu cikakken gindin zama.
Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan an kira ƙarar da EFCC ke neman a ƙwace kadarori guda 57 da ake zargin suna da alaƙa da Malami. Tun da farko dai Mai shari’a Emeka Nwite ne ke kula da shari’o’in a lokacin hutun kotu, kafin babban Alƙali na kotun tarayya, Mai shari’a John Tsoho, ya sake raba ƙarar ga Mai shari’a Egwuatu bayan hutun.
EFCC na tuhumar Malami da laifuka guda 16 da suka shafi zargin halasta kuɗaɗen haram, inda ake zargin kuɗin sun kai Naira biliyan 8.7. Haka kuma, a watan Disambar 2025, hukumar ta ce ta gano kadarori da darajarsu ta kai Naira biliyan 212 da ake alaƙanta su da Malami a jihohin Kebbi, Kano da Babban Birnin Tarayya (FCT). Malami tare da ɗansa da matarsa sun musanta dukkan zarge-zargen da ake yi musu a gaban kotu.
A wata shari’a ta daban kuma, EFCC na neman kotu ta amince da ƙwace kadarori 57 da ake zargin sun samo asali ne daga ayyukan da ba su dace ba. Tun a ranar 6 ga Janairu ne Mai shari’a Nwite ya bayar da umarnin ƙwace kadarorin na wucin gadi, tare da gargaɗin lauyoyi da masu ƙara da kada su nemi tasiri a wajen shari’a ta hanyoyin da ba su dace ba. Yanzu dai ana sa ran za a sake ware wani alƙalin da zai ci gaba da sauraron shari’ar.
