Wani kamfanin tsaro na Amurka, UG Solutions, wanda a baya ya tura tsoffin sojoji ɗauke da makamai domin tsaron cibiyoyin rabon tallafi a Gaza, na tattaunawa da kwamitin “Board of Peace” na Shugaba Donald Trump kan sabuwar rawar da zai taka a yankin.
Kamfanin ya bayyana hakan ne bayan rahotanni sun nuna yana ɗaukar ma’aikata masu iya Larabci da ƙwarewar yaƙi domin aiki a wuraren da ba a bayyana ba. Wata majiya mai masaniya kan shirin kwamitin ta tabbatar da cewa tattaunawar na gudana, ko da yake ba a cimma yarjejeniya ba tukuna.
UG Solutions ya taɓa samar da tsaro ga gidauniyar Gaza Humanitarian Foundation (GHF), wadda Amurka da Isra’ila suka mara wa baya. Sai dai Majalisar ɗinkin Duniya ta soki tsarin rabon tallafin, tana mai cewa ɗaruruwan Falasɗinawa sun mutu yayin ƙoƙarin isa wuraren rabon abinci, a yankunan da sojojin Isra’ila ke sintiri.
Isra’ila ta ce sojojinta sun buɗe wuta ne domin daƙile barazana da tarwatsa cunkoso. Amma ƙungiyoyin agaji sun bayyana tsarin a matsayin mai hatsari kuma ya saɓa wa ƙa’idojin jin kai na ƙasa da ƙasa.
Shugaban cibiyar ƙungiyoyin fararen hula ta Falasɗinu, Amjad al-Shawa, ya ce, “Waɗanda suka tsaya bayan GHF suna da jinin Falasɗinawa a hannunsu; ba a maraba da dawowarsu Gaza.”
Shirin Trump na kawo ƙarshen yaƙin Gaza ya tanadi ƙarin agajin jin kai, janyewar Isra’ila bayan Hamas ta ajiye makamai, da kuma sake gina yankin ƙarƙashin kulawar Board of Peace.
Ana sa ran kwamitin zai yi wani babban taro a Washington mako mai zuwa domin tara kuɗaɗe, ciki har da aiwatar da wani shiri da Jared Kushner ya tsara na sake gina Gaza a matakai, farawa daga Rafah — yankin da GHF ta fi gudanar da ayyukanta.
UG Solutions ta ce ta miƙa shawarwari ga kwamitin, kuma an karɓe su da kyau. Duk da haka, ta ce tana jiran fayyace abubuwan da za su zama fifiko a ɓangaren tsaro kafin yanke hukunci.
Kamfanin ya kuma bayyana cewa kwangilolinsa ba su da alaƙa da umarnin sojojin Isra’ila ko ƙungiyoyin mayaƙa, domin aikinsu ya takaita ne ga tsaron wuraren rabon tallafi kaɗai.
Wannan batu ya sake buɗe babin muhawara mai sarkakiya; ta yaya za a haɗa tsaro mai ɗauke da makamai da kuma ƙa’idojin jin kai?
ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa na kokawa da matsalar satar kayan tallafi da karkatar da su, lamarin da ke sa wasu ke ganin akwai buƙatar tsauraran matakan tsaro. Amma a ɗaya ɓangaren, masu kare hakkin bil’adama na gargaɗin cewa makamai a wurin rabon abinci na iya ƙara janyo tashin hankali da asarar rayuka.
Abin tambayar ana dai ita ce shin tsakanin tsaro na kare al’ummar Gaza daga hare-haren Isra’ila da kuma tsaro na ɓangarorin bayar da tallafi wane yankin ya fi buƙata?
