Sanata Wadada ya jajenta wa kansilolin Nasarawa da suka samu hatsarin mota

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Keffi

Sanatan dake wakiltar mazaɓar Nasarawa ta Yamma a majalisar dattawa ta tarayya wanda har ila yau ɗan takara ne na kujerar gwamnan jihar Nasarawa a inuwar jam’iyyar APC a zaɓen 2027 mai zuwa wato sanata Ahmed Aliyu Wadada ya bayyana alhinin sa dangane da wani labarin baƙin ciki da yace ya samu na wani mummunar hatsari da ya rutsa da wasu kansilolin ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar ta Nasarawa wanda ya auku a hanyar Alushi dake ƙaramar hukumar Akwanga a lokacin da kansilolin ke tafiyar wani aiki a hukumarce inda sanatan ya ƙara da cewa tabbas hatsarin ya ruɗa shi matuƙa.

Sanata Aliyu Ahmed Wadada ya bayyana haka ne a wata sanarwa wanda mai taimaka masa na musamman na labarun yanar gizo, kwamared Victor Akawu ya sanya hannu a ka raba wa manema labarai a birnin Keffi jim kaɗan bayan aukuwar lamarin.

Sanarwar ta cigaba da bayyana cewa ” Duk da tashin hankali da aukuwar a tsarin ya jawo wa al’umma, mai girma Sanata Ahmed Aliyu Wadada yana miƙa godiya na musamman ga Ubangiji Allah game da rahamar sa musamman yadda labarin ya kasance cikin sauƙi ba a rasa rayuka ba sakamakon mummunar hatsarin.

“Tabbas wannan kariyar Allah yana nuni cewa a ko yaushe Allah yana tare da al’ummar sa.

“A wannan halin juyayi, Sanata Ahmed Aliyu Wadada yana addu’a da fatan Allah ya cigaba da tausaya wa waɗanda lamarin ya shafa da iyalansu yana kuma addu’ar Ubangiji ya basu sauƙin warkewa daga raunuka da suka samu cikin gaggawa.” Kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Wakilin mu a jihar ta Nasarawa John Dogo Wada ya kuma rubuto cewa ɗan siyasar wanda aka san shi da aikin agaji da tausayi irin wannan wato Sanata Ahmed Aliyu Wadada daga nan sai ya kuma yi amfani da damar inda ya kuma roƙi Allah ya cigaba da kare al’ummar jihar Nasarawa da ƙasar Najeriya baki ɗaya musamman daga ire-iren wannan bala’i da masifa da sauran su.

By ukarofi