Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Tsohon Gwamnan jihra Kano, tsohon shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yaba wa babban Darakta na kadarorin Gwamnatin tarayya Hon. Aminu Muktar ɗan’amu bisa kayayyakin abinci da ya shirya na taimakawa marayu da sauran al’umma da cewa abu ne da ya yi shi a daidai lokacin da “karaya ce ta zo daidai da gaɓa” a watan Azumi domin abinda za a ci a gida yana da muhimmanci kuma sai gashi ya yi wannan tanadi da ba a san yawan al’umma da zasu ci gajiyar wannan taimako ba.
Ya yi nuni da cewa duk wanda zasu karɓi tallafin abincin wakilai ne kawai na waɗanda za su buɗe baki suci wannan abinci saboda haka ya roƙi masu cin gajiyar abincin in sun yi azumi su yiwa Aminu Muktar ɗan’amu addu’a dama shi daga sunansa kasan daga inda yake ɗan gidan malamai ne masu daraja. Ya godewa Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda ya turo Kwamishinan sa na yaɗa labarai Ibrahim Waiya taron raba tallafin.
A nasa jawabin shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano .Alhaji Abdullahi Abbas ya godewa Hon. Aminu ɗan’amu bisa irin abinda ya yi wanda ya yi daidai da tafiyarsu ta siyasa kuma a matsayinsu na shugabannin jam’iyyar APC a Kano ya burge su kuma ya ce duk wanda yake da mulki a ƙarƙashin APC zaɓaɓɓe ko naɗaɗɗe lallai ne ya yi irin wannan tallafi a cikin watan azumi duk kuma wanda yake son takara baya taimakon mutane baya bai wa marayu abinci ba shi ba bu samun lasisin takara a APC. Damar takara shine mai ka yiw a jama’a.
Shi ma a nasa jawabin kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano.Ibrahim Waiya ya bayyana cewa wannan rabon tallafin kayan abincin da Hon.Aminu Muktar ɗan’amu yayi daidai ne da abinda Gwamnan Kano Abba kabir Yusuf yake yi domin tausayawa al’umma da kuma marayu ko a shekarar da ta gabata a watan Azumi ya sahale aka ƙirƙiri cibiyoyi da ake ciyar da dubban mutane ana ciyar da mutum dubu 91 a kullum tareda raba kayan abinci da mabukata .
Tun da farko a jawabinsa Hon.Aminu Muktar ɗan’amu babban darakta na hukumar kula da kadarori”Asset management cooperation”Tsohon kwamishinan kuɗi a gwamnatocin Kwankwaso da na Ganduje a jihar Kano ya ce za a raba tallafin kayan abinci ga gidajen marayu 501 da yan sisaya na ƙaramar hukuma Birnin Kano.
Ya kuma nuna godiya ga Allah da ya bashi dama ya yi amfani dashi wajen wannan tallafi da ya yiwa marayu wanda dama can ya saba yana yi a baya ba tare da bayyanawa ba,amma a wannan lokaci aka bada shawarar yakamata ayi yanda za a gani don wasu suyi koyi da abinda ake don ko zakka ma ance ana so a bayyana saboda wasu su tuna suma haƙƙi ne akansu.
Ya ce gidajen marayu 501 ne aka baiwa tallafin wanda shine ɗaya da aka ɗora a cikin 500 ɗin saboda shima maraya ne.A baya da suke yara yakan iya tuna idan baƙi sun zo unguwar su babu mai kwana da yunwa saboda mutane ana dunƙule ana taimakekeniya kuma in akace a rayuwa wani ya kwana bai ci abinci ba masu hali gaba ɗaya suna da laifi saboda Ubangiji ya baiwa wasu wadata da zasu tallafa sai dai in basu yi abinda yakamata ba.
Hon. Aminu Muktar ɗan’amu ya yi kira da mutane da suka amfana da tallafin idan suka koma gidajensu suma su ɗauki ɗan wani abu su taimaki wanda yake kusa dasu idan ka samu buhun shinkafa ka samu maƙocinka ka ba shi ko da kwano ɗaya ko biyu ne kai ma za ka ga buɗi.
