
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A halin yanzu wani tsohon bidiyon Shugaba Bola Tinubu da sabon Sufeto Janar na rundunar ‘yan sanda, Tunji Disu da aka ɗauka tun a shekarar 2001 na karaɗe shafukan sada zumunta.
Ɗaukar ta nuna daidai lokacin da Shugaba Tinubu ke amsa tambayoyin ‘yan jarida a lokacin da yake gwamnan Legas, yayin da shi kuma Disu yake aiki a matsayin babban dogarin, wato ADC a bayansa.
A jiya Laraba, 25 ga Fabarairu, 2026 ne Tinubu ya ƙawata Disu da shigar muƙamin sufeto janar na ‘yan sanda a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
An gudanar da taron ne da misalin karfe 4 na yamma a ofishin shugaban ƙasar, wanda ya samu halartar Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu; Shugaban Ma’aikatan Fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila; Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da kuma tsohon Sufeto Janar kai barin gado, wato Kayode Egbetokun.
Shugaba Tinubu ne da kansa ya manna tambarin girmamawa ga Disu yayin da ya kuma yi jinjina ga Egbetokun bisa hidimarsa a muƙamin.
An naɗa Disu a muƙamin ne kwanaki 48 da lokacin kammala aikinsa zai cika a ranar 13 ga Afrilu, 2026, inda kuma a lokacin ne zai cika shekaru 60 na yin ritaya.
To saidai duk da haka, ana ganin akwai yiwuwar ya yi hidimar karin wasu shekaru huɗu bisa la’akari da gyaran fuska da aka yi dokokin ‘yan sanda.
