Ma’aikatar al’amuran addini a Yobe na bibiyar ciyarwar watan Ramadan

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN, Damaturu

Tun a farkon watan Ramadan ne Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya amince da kashe kimanin Naira miliyan 398 a shirin ciyarwa a watan Ramadan na wannan shekara ta 2026, tare da tallafa wa tafsirin da malamai ke gudanarwa a faɗin jihar.

Yayin da yake ƙaddamar da shirin ciyarwa, Kwamishina a ma’aikatar al’ammuran addini da ɗa’a da wayar da kan jama’a, Alhaji Yusuf Umar, ya yaba wa Gwamna Buni da ci gaba da faɗaɗa shirin.

Haka kuma, Kwamishinan ya bayyana shirin a matsayin yar manuniya dangane da sadaukarwar gwamnati wajen kula da jin daɗin marasa galihu, al’amarin da yake kawo sauƙi ga masu ƙaramin ƙarfi a faɗin jihar.

Har wala yau, Alhaji Yusuf ya buƙaci mambobin kwamitocin ayyukan ciyarwar a cibiyoyi daban-daban a faɗin jihar, su kula tare da riƙe amana wajen sauke amanar da aka damƙa musu.

Haka zalika kuma ya yi kakkausan gargaɗi game da karkatar da kayan abincin ko kuma rashin kula da su, inda ya umarci dukkan jami’ai da su bi ƙa’idojin gwamnati sosai don tabbatar da gaskiya da kuma nasarar aiwatar da shirin.

Wannan shi ne karon farko wanda ma’aikatar za ta aiwatar da gagarumin aikin ciyarwar fiye da na shekarun baya, wanda a wannan karon, gwamnatin jihar Yobe ta ƙara yawan wuraren ciyar da mutane daga 101 zuwa 130, wanda hakan ya tabbatar da kaiwa ga dukkan ƙananan hukumomi 17.

An tsara kowace cibiya za ta rinƙa ciyar da mutane 100 abincin buɗa- baki a kowace rana a tsawon lokacin azumin, wanda hakan zai tallafa wa dubban masu ƙaramin ƙarfi samun abincin buɗa- baki a kowace rana.

A cikin wannan adadi na Naira miliyan 338, za a siya raguna da kayan abinci na wuraren ciyarwar, wanda ya haɗa da ware Naira miliyan 60 don alawus-alawus ga malaman addinin Musulunci da za su jagoranci tafsiri a faɗin jihar Yobe.

Haka kuma, gwamnatin jihar Yobe ta amince da raba buhunan shinkafa 2,300 da galan 400 na man girki a waɗannan cibiyoyi 130.

By ukarofi