Kano: Hisbah ta kama matasa biyu kan zargin shirya bikin zagayowar ranar haihuwa na ‘yan daudu

Spread the love

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu matasa da ake zargi da maida kansu ‘yan daudu tare da shirya wani biki na “sheke aya”, inda har suka gayyaci shugabannin Hisbah zuwa taron.

Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Mujahideen Aminudeen, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai.

A cewarsa, mutanen da aka kama sun hada da Umar Yahya mai shekara 19 da Musa Alhassan mai shekara 18, waɗanda sun mayar da kansu ‘yan daudu tare da jawo wasu daga cikin abokansu maza su shiga irin wannan hali.

Sheikh Mujahideen Aminudeen ya kara da cewa matasan sun shirya wani bikin zagayowar ranar haihuwa (birthday), inda suka gayyaci wasu ‘yan uwansu ‘yan daudu domin gudanar da shagulgula da abubuwan da suka sabawa tarbiyya a lokacin bukukuwan Sallah.

Ya ce bayan samun bayanan sirri kan shirin bikin, jami’an Hisbah sun kai samame tare da kama wadanda ake zargin.

Mataimakin babban kwamandan ya bayyana cewa matasan da aka kama ba su da cikakken ilimin addini kuma ba su da sana’ar yi, yana mai cewa irin wadannan dabi’u ne ke jefa matasa cikin matsaloli a cikin al’umma.

Ya kara da cewa hukumar Hisbah za ta tsare su na wani lokaci domin koya musu ilimin addini tare da horas da su sana’o’in dogaro da kai.

A nasu bangaren, matasan da aka kama sun nemi afuwar hukumar tare da yin alkawarin cewa ba za su sake aikata irin wannan laifi ba, suna kuma fatan a yafe musu.

By Babaji