Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ɗage shari’ar rikicin babban taron PDP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Laraba Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zaune a Ibadan ta dakatar da shari’ar jam’iyyar PDP da ta ƙunshi batun zaɓen babban taron da ta yi birnin a shekarar da ta gabata.

Haka kuma kotun ta nemi ɓangarorin da ke rikicin akan al’amarin da su sulhunta kansu a waje da kotu.

A yayin hukuncin akan shari’ar, tawagar alƙalan kotun ta yi kira ga ɓangarorin da su zaɓi warware matsalolin da ke tsakaninsu ta lumana.

A cewar kotun matuƙar suka kasa cimma yarjejeniya, to suna da damar sake garzayawa kotu domin yanke hukunci a tsakaninsu.

Sannan kotun ta gargaɗi lauyoyi da su riƙa kula da lokaci bisa la’akari da sabon jaddawalin zaɓen 2027 da Hukumar Zaɓe (INEC) ta fitar.

A kwanan nan ne Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja ta ayyana babban taron, wanda aka zaɓi Kabiru Turaki a muƙamin shugaba, a matsayin haramtacce.

A yayin shari’ar ƙarƙashin jagorancin alƙalai uku na kotun, sun yanke cewa ɗaukaka ƙara da PDP ta yi ba shi da nagarta, lamarin da ya sa ta tabbatar da hukuncin Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya ta Abuja da aka yi a ranar 3q ga Oktoba.

By Babaji