
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya gayyaci dukkan jagororin rundunonin soji zuwa ofishinsa domin wani taro na gaggawa akan hare-haren da aka kai kwanan nan a sansanonin soji daban-daban a yankin Arewa maso Gabas.
Waɗanda suka halarci taron, wanda aka gudanar a Hedikwatar Ma’aikatar Tsaro da ke Abuja a yau Laraba, sun haɗa da Shugaban Hafsoshin Tsaro, Olufemi Oluyede, da Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, Waidi Shaibu.
Sauran sune Shugaban Rundunar Sojin Sama, Sunday Aneke; Shugaban Rundunar Sojin Ruwa, Idi Abass; da wakilai daga Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa da dai sauransu.
A ‘yan kwanakin nan, ‘yan ta’adda sun halaka aƙalla manyan jami’an soja uku masu muƙamin Laftanal Kanal a Jihar Borno.
Haka kuma, sojoji da dama ma sun rasa rayukansu yayin da aka sace ɗaruruwan fararen hula waɗanda har yanzu ke hannun ‘yan ta’adda.
Christopher Musa ya ce sun amince su sake duba dabarun yaƙi da ‘yan ta’adda a sassan ƙasar.

