
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sabon jagoran addinin ƙasar Iran, Mojtaba Khamenei ya samu raunuka sakamakon yaƙin yankin Gabas ta Tsakiya da ke cigaba da gudana, amma yana nan cikin ƙoshin lafiya, kamar yadda ɗansa Yousef Pezeshkian ya sanar.
Sanarwar, wadda aka yi a yau Laraba ta nuna cewa wannan shi ne karo na farko da aka ga shugaban mai shekaru 56 ya ƙaurace wa bainar jama’a tun bayan naɗa shi da aka yi a ƙarshen makon da ya gabata.
Pezeshkian, wanda kuma mai ba gwamnatin ƙasar shawara ne, ya tabbatar da haka ta kafar Telegram sakamakon yaɗa rahotanni akan jikkata da shugaban ya yi.
An naɗa Mojtaba Khamenei, wanda jigo ne na ɓoye a harkokin siyasar Iran, a matsayin jagoran addinin ƙasar bayan yaƙin da Amurka/Isra’ila ke yi da Iran ya yi ajalin mahaifinsa, Ali Khamenei.
Saidai ba a samu fitar da bayanan matakin raunin da shugaban ya samu ba, duk da cewa New York Times ta ruwaito cewa daga cikinsu akwai na ƙafafunsa.
