Daga IBRAHIM MUHAMMADU a Kano
Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Kano kuma tsohon Kwamishinan Sufuri, Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda aka gudanar da zaɓen sabbin shugabannin jam’iyyar a jihar.
Namadi Dala ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, inda ya ce zaɓen da aka gudanar wanda ya samar da sabon shugabanci ƙarƙashin Hon. Umar Haruna Doguwa ya gudana cikin fahimtar juna, haɗin kai da kuma kwanciyar hankali.
Ya taya dukkan sabbin shugabannin jam’iyyar da aka zaɓa daga matakin mazaɓu zuwa ƙananan hukumomi da kuma matakin jiha murna, yana mai cewa yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana alama ce ta karfin jam’iyyar a jihar.
A cewarsa, yadda aka gudanar da zaɓen ya nuna cewa jam’iyyar APC na da karfi a Kano, kuma hakan zai taimaka wajen samun nasara a zaɓen shekarar 2027, musamman ganin cewa Kano na daga cikin manyan cibiyoyin siyasa a Nijeriya.
Namadi Dala ya kuma yaba wa manyan jagororin jam’iyyar APC a jihar Kano bisa haɗin kai da suka nuna wajen tabbatar da nasarar zaɓen shugabannin jam’iyyar.
Ya ambaci wasu daga cikin jagororin da suka taka rawa wajen ganin an samu wannan nasara da suka haɗa da tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da kuma Sanatan Kano ta Arewa kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin.
Ya kuma bayyana Hon. Umar Haruna Doguwa, sabon shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, a matsayin mutum mai kwarewa da jajircewa wajen gudanar da ayyukan da aka dora masa.
A cewarsa, Doguwa ya taba rike mukamai daban-daban a baya kuma ya nuna kwarewa wajen gudanar da su, don haka yana da yakinin cewa zai yi aiki tukuru domin karfafa jam’iyyar APC a jihar Kano.
Namadi Dala ya yi kira ga dukkan ‘yan jam’iyyar APC a Kano da su bai wa sabbin shugabannin jam’iyyar goyon baya, domin tabbatar da haɗin kai da kuma ƙarfafa jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.
A ƙarshe, ya bayyana fatan cewa idan lokacin zaɓen ‘yan takara ya zo, za a gudanar da shi cikin haɗin kai da fahimtar juna, tare da bai wa duk wanda ya yi nasara cikakken goyon baya domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zabuka masu zuwa.
