Daga RABIU SANUSI a Kano
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) ta miƙa takardar shaidar cin zaɓe ga Hon. Ali Musa “Hardworker,” inda ta tabbatar da shi a matsayin halastaccen Shugaban ƙaramar Hukumar Kumbotso, biyo bayan umarnin kotu.
Yayin miƙa takardar, Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Lawal Malumfashi, ya bayyana cewa hukumar na aiki ne bisa tanadin doka wajen gudanar da zaɓe da kuma bayyana waɗanda suka yi nasara a matakai daban-daban.
Ya ce matakin da aka ɗauka ya biyo bayan hukuncin kotu ne wanda ya tabbatar da Hon. Ali Musa Hardworker a matsayin wanda ya lashe zaɓen, bayan doke abokin hamayyarsa, Hon. Ghali Basaf.
“Mun bi umarnin kotu ba tare da kaucewa ba, domin hakan ne ya dace da aikinmu a matsayin hukuma mai zaman kanta,” inji Malumfashi.
A nasa jawabin, Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa, ya jaddada muhimmancin girmama dokoki da hukuncin kotu domin tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya.
Ya kuma yabawa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda take ƙarfafa bin doka da oda, yana mai cewa hakan na taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Doguwa ya buƙaci sabon shugaban ƙaramar hukumar da ya rungumi shugabanci mai haɗa kai tare da kawo ci gaba ga al’ummar Kumbotso.
A nasa bangaren, Hon. Ali Musa Hardworker ya nuna godiya ga Allah tare da bayyana nasarar a matsayin ta adalci da kuma dawo da haƙƙin jama’a.
Ya ce, “Wannan rana babbar rana ce ga al’ummar Kumbotso. Nasara ce ta gaskiya da muradin masu zaɓe.”
Hardworker ya yi alƙawarin bai wa gwamnatin jihar cikakken goyon baya tare da yin aiki tukuru domin ci gaban yankin, yana mai tabbatar da cewa al’ummar Kumbotso za su ci gaba da mara wa gwamnati baya.
Lamarin ya sake nuna muhimmancin rawar da bangaren shari’a ke takawa wajen warware rikice-rikicen zaɓe da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya a Najeriya.
