
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba Shugaba Bola Tinubu ya sanar da dakatar da shirinsa na tafiya Iperu da ke Jihar Ogun, inda ya bayyana cewa a halin yanzu babban aikinsa shi ne tsayawa tare da al’ummar Jihar Filato sakamakon hare-haren da suka yi sanadiyyar asarar rayuka da dama.
A sanarwar da ya fitar, Shugaban ƙasar ya ce zai ziyarci birnin Jos domin jajenta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu, tare da sake jaddada cewa masu ƙoƙarin tayar da zaune-tsaye a ƙasar ba za su yi nasara ba.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta cigaba da ƙarfafa matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da cewa an hukunta masu hannu a hare-haren.
Don haka, madadin tafiya kudu a yanzu, Tinubu ya ɗage tafiyar zuwa ranar Asabar, 4 ga watan Afrilu domin ƙaddamar da filin jiragen sama da wasu jiragen ‘yan kasuwa na sufurin kayayyaki domin bunƙasa harkokin kasuwancin jihar.
Baya ga haka, shugaban ƙasar zai ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan ci-gaba a jihar da suka haɗa sashen ayyana Hukumar Kwastom da motocin ayyukan jami’anta.
