
Shugaban tsagi na jam’iyyar ADC na ƙasa, Nafi’u Bala ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi murabus daga muƙaminsa na mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Bala ya bayyana cewa, takardar murabus ɗin da ake yaɗawa ba tasa ba ce, yana mai zargin cewa an ƙirƙiri sa hannunsa domin yaɗa rikici a cikin jam’iyyar. Ya jaddada cewa har yanzu yana kan kujerarsa, kuma bai ajiye aiki ba ko kaɗan.
Wannan martani nasa na zuwa ne bayan hukuncin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta yanke a ranar Laraba, dangane da rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar ADC.
Rikicin cikin gida a jam’iyyar ADC dai na ci gaba da ɗaukar sabon salo, inda ɓangarori daban-daban ke fitar da matsayinsu kan shugabancin jam’iyyar, lamarin da ke janyo cece-kuce a tsakanin magoya baya da ‘yan siyasa.
