Kotu ta yanke wa matashi hukuncin rataya a Gombe

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Babbar Kotun Jihar Gombe mai lamba 2 ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi mai shekaru 18, Mustapha Adamu Isah, wanda aka fi sani da Abbati, bayan ta same shi da laifin kashe wata mata mai shekaru 58 mai suna Aishatu Abdullahi, wadda aka fi sani da Damori.

Mai shari’a Abdulhamid Mohammed Yakubu ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba.

Kotun ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 20 ga Oktoba, 2023, da misalin karfe 9:00 na dare a unguwar Jekadafari da ke Gombe.

An ce wanda aka yanke wa hukunci, mazaunin titin Santana, ya shiga gidan marigayiyar ba bisa ka’ida ba, inda ya yi mata yankan rago da wuka, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.

Daraktan Sashen Gurfanar da Kara na gwamnati, Barista Abubakar Jungudo, ya shaida wa kotu cewa laifin ya saba wa Sashe na 220 na Dokar Penal Code, kuma hukuncinsa yana karkashin Sashe na 221.

Duk da cewa wanda ake tuhuma ya musanta laifin, masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu da hujjoji domin tabbatar da zargin.

Lauyan da ke kare wanda ake tuhuma, Barista Adamu Abdulkadir, ya yi wa shaidun tambayoyi domin kalubalantar su. Sai dai a hukuncinsa, Mai shari’a Yakubu ya dogara da shaidun da aka gabatar da kuma bayanin wanda ake tuhuma, inda ya tabbatar da cewa laifin da gangan aka aikata shi kuma ya jawo mutuwar marigayiyar.

Daga bisani, kotun ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya kamar yadda doka ta tanada.

By ukarofi