Karancin wutar lantarki da tsadar gas ya kawo rashin armashi a bukukuwan Sallah a Legos da Ogun

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Al’ummar jihohin Legos da Ogun sun shiga cikin mawuyacin hali yayin da matsalar rashin wutar lantarki da tashin farashin gas ɗin girki suka dabaibaye shirye-shiryen bikin Sallah.

Rahotanni sun nuna cewa yankuna da dama da ke ƙarƙashin kamfanonin rarraba wutar lantarki na Ikeja da Ibadan DisCos sun shafe kusan kwanaki huɗu ba tare da wuta ba, ciki har da Ojodu, Berger, Ogba, Ketu, Arepo, Magboro, Mowe da Ibafo.

Kamfanin Ikeja Disco ya sanar da abokan hulɗarsa cewa matsalar ta samo asali ne daga lalacewar layukan wuta da kuma matsala a tashar rarraba wuta, yana mai cewa ana ƙoƙarin gyarawa domin dawo da wutar cikin gaggawa.

Baya ga rashin wutar lantarkin, mazauna yankunan sun kuma koka kan tashin gwauron zabo da farashin gas ɗin girki ya yi daga N1,500 zuwa tsakanin N2,000 da N2,200 kan kowanne kilo a daidai lokacin bukukuwan Sallah.

An ga mutane da dama suna yawo daga wani wurin sayar da gas zuwa wani suna neman inda za su samu mai rahusa, yayin da wasu gidajen sayar da gas suka rufe saboda matsalar ƙarancin sa.

Wasu mazauna yankunan sun bayyana cewa sun koma amfani da gawayi domin girki sakamakon tsadar gas ɗin.

By ukarofi